Wani hafsan dan sanda kwantar da tarzoma mai mukamin Sufeto ya bindige kansa jim kadan bayan dawowarsa daga wurin aiki.
Wani ganau ya ce sai da hafsan dan sandan kwantar da tarzoman ya kulle kansa sannan ya dirka wa kansa harbi da ciki wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa a ranar Laraba.
- Ba’amurkiyar da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu
- Dubun masu kwacen waya a Kano ta cika
- Bidiyon tsiraici: Dan hadimin Tambuwal ya gurfana a kotu
- An kama mijin malama yana mata satar jarabawa
“Da ’yan sandan kwantar da tarzoma suka dawo aiki sai ya shige wani daki ya kulle; bayan ’yan mintoci sai muka ji karar harbi a dakin.
“Mun yi kokarin shiga dakin amma sai muka iske kofar a kulle; Da aka balla kofar muka shiga sai muka samu dan sandan a kwace cikin jini rai ya yi halinsa,” inji shi.
Ya ce abin da ya faru da Sufeton dan sandan da ke aiki a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Owerri Jihar Imo, ya haifar da fargaba a yankin.
Mutumin ya ce duk da cewa a dan sandan ya koka cewa yana fama da rashin lafiya, amma babu wanda ya yi zaton zai kashe kansa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Nasiru Muhammed, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin kisan.