✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani basarake ya raba wa matasa Keke Napep 25 a Bauchi

Wani basarake ya raba wa wasu matasa Keke Napep 25 a kwanakin baya a garin Azare da ke jihar Bauchi. A wani mataki na samar…

Wani basarake ya raba wa wasu matasa Keke Napep 25 a kwanakin baya a garin Azare da ke jihar Bauchi. A wani mataki na samar wa matasa ayyukan yi don magance  zaman kashe wando.
A zantawarsa da Aminiya basaraken mai suna Injiniya Abubakar Azare, Tafarkin Nasarawa ya ce samar wa matasa sana’o’i  shi ne babbar hanya da za ta taimaka wajen samun zaman lafiya tsakankanin al’umma.
Ya ce: “Na raba ababan hawan ne akan farashi mai sauki ga matasan don su iya dogara da kansu, su yi watsi da zaman banzan da ke haddasa zaman daba ko majalisa.”
Ya kara da cewa, “a halin da kasar nan ke ciki musamman yankin arewa, hali ne da ke bukatar da karatun ta nutsu domin kuwa al’ummar yankin na cikin halin kuncin rayuwa musamman matasa wadanda su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, domin duk al’ummar da aka ce dimbin matasanta na zaune  ba su da aikin yi, to ya zama lalle ta san cewar tana cikin halin rashin tabbas.
Don haka a cewar sa hakan ne ya sa yaga ya dace da ya taimaka matuka kan wannan tafarki don ganin ya rage zaman banzan da matasa ke yi duk da cewar ya fara wannna yunkuri ne tun daga iyalensa yadda ya samar musu keke napep ga kowace iyalinsa don su rika biyan bukatar kansu ba sai sun tinkare shi ba, to shine da yaga lamarin na habaka sai ya yi tunanin sake sayo Babura ma su tayoyi ukun don  rarrabawa ga wasu matasan don su ma su dogara da kansu.”
Basaraken ya roki ma su hannu da shuni da su yunkuro domin ba da gudunmawarsu ta wajen samar wa da matasa aikin yi. Ya ce “ba wai sai hukuma kawai ba. Kowa zai iya taimakwa wadda hakan kuma zai yi matukar rage irin tashin tashinar da ake yawaita samu a cikin al’umma. Amma matukar ba hakan aka yi ba to kuwa ko shakka babu daga baya matasan ba abin da zai hana su fada wa ma masu hannu da shuni don samar wa kansu abin biyan bukata ta bin mummunar hanyar da ke da alaka da ta’addanci.
Tafarkin na Nasarawa ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba wannan aikin kuma ya ce yana yi ayyukan sa ne tsakani da Allah ba don wani burin siyasa da yake da shi ba.