✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani Basarake ya auri kada

Mutanen kauyen suna alakanta macen kadan a matsayin mai wakiltar uwa ta duniya.

Magajin garin wani kauyen masu sana’ar kamun kifi a Mexico ya auri kada, inda a ranar auren aka sanya wa kadar farar rigar aure, irin ta amare.

Magajin garin mai suna Victor Hugo Sosa da masoyiyarsa sun sunbaci juna a ranar aurensu tare da gudanar da wasu abubuwa na al’ada.

Bikin ya gudana ne a birnin San Pedro Huamelula da ke Mexico.

Macen kadan mai shekara bakwai, wacce ake yi wa lakabi da ‘Karamar Gimbiya,’ an daure hancinta domin kada ta yi kokarin gudu.

A al’adance, mutanen kauyen suna alakanta macen kadan a matsayin mai wakiltar uwa ta duniya kuma sun fassara auren a matsayin alamar haduwa abin abin bautarsa.

Al’adar auren kada ta samo asali ne tun kafin karni na 16, tsakanin al’ummomin Chontal da Huabe a cikin Jihar Oadaca da ke Kudu maso Yammacin Mexico.

An yi ta kade-kade da wake-wake na gargajiya yayin da masu shagulgulan suka rika raye-raye a a ranar bikin.

“Muna rokon yanayi mai kyau don samun isasshen ruwan sama, domin samun isasshen abinci, wato kifi a cikin kogin,” inji Sosa.

Jihar Oaxaca ta kasance gida ce ga mutane ’yan asalin kasar da yawa wadanda suke daraja kiyaye yarensu da al’adunsu.

Al’ada a birnin San Pedro Huamelula kuma ta yarda da darikar Katolika kuma ta amince da yin sutura ga kadar a cikin farar riga a bikin aure.

Mazauna yankin sun dauki amaryar a hannunsu ta hanyar bin titin kauyen yayin da mazaje ke ta yi mata fifita da huluna mai malafa.

“Yana ba ni farin ciki sosai kuma yana sa ni alfahari da asalina,” inji Elia Edith Aguilar, wacce aka fi sani da uwar baiwa, wacce ta shirya bikin auren.

Ta bayyana jin dadinta da yawa don gudanar da bikin kuma ta amince da ba da lokacinta mai yawa don kula da kayan amarya.