Ya bayin Allah! Hakika Allah Ya yi mana rahama mayalwaciya sakamakon kebe mu da sanya mu mabiya mafi alherin halitta (SAW), wanda ya fitar da mu daga duffan kafirci da zalunci zuwa ga hasken imani, ya fitar da mu daga bata zuwa ga shiriya ya fitar da mu daga tabewa zuwa ga sa’ada daga kaskanci da zalunci da jahilci da rarrabuwa da wulakanci zuwa ga daukaka da adalci da haduwar kai da karimci. Shin yaya za mu kasance ba domin addinin Annabi Muhammad da akidarsa ba? Wace kima za mu yi in ba domin sakonsa da shari’arsa ba? Wace makoma muke da ita in ba domin da’awarsa da akidarsa ba? “Lallai ne hakika, Allah Ya yi babbar falala a kan muminai, domin Ya aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littafi da hikima, kuma lallai sun kasance daga gabani, hakika suna cikin bata bayyananniya.” (K:3:164).
Ya isar da sako mafi kyawun isarwa, ya bayar da amana, kuma ya yi nasiha ga al’umma, kuma ya yi kokari a cikin yada addinin Allah iyakar kokarinsa. Mutanensa sun cutar da shi, amma ya yi hakuri domin ya isar da wannan sako. Ya tafi zuwa Da’ifa da kafa yana mai gabatar da Musulunci ga kabilunta, amma suka sanya kananan yaransu suka rika jifarsa suka raunata shi a kafarsa amma ya yi hakuri don isar da da’awar. Ya rika zuwa ga kabilun Larabawa amma suna korarsa, sai dai irin wannan bai kashe masa gwiwa ba. An rika azabtar da sahabbansa a cikin zafin rana suna masu igasa da neman tyaimako da Allah Madaukaki saboda wannan addini. Har ta kai an umarce shi da hijira daga birnin Makka inda ya tsaya a wajen Makka yana mai cewa: “Wallahi ke ce mafi soyuwar bigire zuwa ga Allah. Kuma wallahi ke ce mafi soyuwar bigire a wurina, ba domin mutanenki sun fitar da ni ba, da ban fita ba.”
Wata rana an fasa masa kai, an karya masa hakoran gaba, makiya sun yi yunkurin kashe shi a yakin Khandak, inda suka tura rundunoni domin neman kansa. Yahudawa sun sanya masa guba a abinci, sun yi masa sammu, sun yi kokarin kashe shi a lokuta da dama. Sai dai wannan bai sanyaya azamarsa ta yada wannan addini ba, har sai da Musulunci ya isa mahudar rana da mafadarta.
Ba za a iya kirga falalolinsa ba, kuma martabobinsa ba za su kididdigu ba. Babu wata siffar kamala face ya siffatu da ita, Allah Ya tsarkake hankalinsa inda Ya ce: “Ma’abucinku bai bata ba, kuma bai ketare haddi ba.” (K:53:2). Kuma Ya tsarkake harshensa inda Ya ce: “Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa.” (K:53:3). Kuma Ya tsarkake shari’arsa inda Ya ce: “(Maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne da ake aikowa.” (K:53:4). Kuma Ya tsarkake mai karantar da shi inda Ya ce: (Mala’ika) mai tsananin karfi ya sanar da shi. Ma’abucin karfi da kwarjini, sa’an nan ya daidaita.” (K:53:5-6). Kuma Ya tsarkake zuciyarsa inda Ya ce: “Zuciyar (Annabi) ba ta karyata abin da ya gani ba.” (K:53:11). Kuma Ya tsakake ganinsa inda Ya ce: “Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ketare haddi ba.” (K:53:17). Kuma Ya tsarkake sahabbansa inda Ya ce: “Kuma wadannan da suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu.” (K:48:29). Kuma Ya tsarkake shi gaba dayansa inda Ya ce: “Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki manya.” (K:68:4).
Kuma Ya jingina shi da risala inda Ya ce: “Muhammadu Manzon Allah ne.” (K:48:29). Kuma Ya kira shi da sunan annabta inda Ya ce: “Ya kai Annabi!” (K:60:12). Kuma Ya daukaka shi da bauta inda Ya ce: “Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi tafiyar dare da bawanSa.” (K:17:1). Kuma Ya yi masa shaida da tsayuwa da ibada inda Ya ce: “Kuma lallai ne shi a lokacin da bawan Allah ya tsayu yana kiranSa.” (K:72:19).
Allah Ya budada masa kirjinsa Ya dauke masa nauyinsa, Ya daukaka ambatonsa Ya cika al’amarinsa Ya kammala addininsa, Ya sanya damarsa mai da’a. Ubangijinsa bai yi masa ban-kwana ba, kuma bai ki shi ba. Sai dai ya same shi ba ya da shari’a, sai Ya shiryar da shi. Ya same shi fakiri Ya wadatar da shi. Kuma Ya same shi maraya Ya yi masa makoma. Ya ba shi zabi tsakanin dauwama a duniya da haduwa da Shi, sai ya zabi haduwa da Majibincinsa ya ce: “Na zabi haduwa da Madaukaki.”
“Na rantse da Allah wata mace ba ta yi ciki ko ta haifi, kamar Manzo,
Annabin al’umma mai shiryarwa ba.”
Sai ga shi wata rana ta zo, wadansu mutane da ba su san Allah ba koda daidai da sa’a daya suna rayuwa cikin duffan sha’awoyi, manufofinsu da tunaninsu da akidojinsu batattu suna kokarin karkata daga wannan haske.
Misali a shekarun baya, wata jaridar Denmark da sauransu sun buga zanen hoto na isgilanci ga mafificin halitta daukacin Musulmi na ji na gani, ina kishin addinin? Ina son Manzon (SAW)? Ina kare shi? Ashe ba wannan ne matsayin shugabanmu Manzon Allah (SAW) ba?
Wadannan Allah zai yi musu kamun ramuwa, domin Ya ce a cikin LittafinSa: “Kuma Allah Yana tsare ka daga mutane.” (K:5:67). Utbah dan Abu Lahabi ya cutar da shi ya yi masa isgili, sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka shushuta masa wani kare daga cikin karnukanka.” Sai ya zamo bai iya barci sai a tsakiyar ’yan uwansa saboda tsoron addu’ar Manzon Allah (SAW), amma wannan bai kare shi ba, domin a daya daga cikin tafiye-tafiyensa sai ya farka ya ga mafadacin zaki ya sanya faratunsa a muka-mukinsa, sai ya fasa ihu yana cewa: “Ya ku mutanena! Addu’ar Muhammad ta kashe ni.” Kuma wannan bai wadatar da shi da komai ba.
Kisra ya keta wasikarsa sai ya yi masa addu’a, sai Allah Ya hallaka shi a zamaninsa, Ya kekketa mulkinsa kekketawa, mulki bai sake komawa hannun Kisrawa ba a bayansa, domin tabbatar fadinSa Madaukaki: “Lallai mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka.” (K:108:3). Domin haka duk wanda ya zage shi ko ya tozarta shi ko ya nakasa shi ko ya yi gaba da shi, to lallai Allah zai karya kashin bayansa Ya debe albarka a idonsa da zuriyarsa. Ya zo a cikin Sahihu daga Annabi (SAW) cewa lallai ya ce: “Allah Madaukaki Yana cewa, duk wanda ya yi adawa da wani waliyiNa, hakika Na yi masa izini da fafata yaki da Ni.” To yaya kuma wanda ya yi adawa da Shugaban Annabawa (AS)?
Allah Ma’abucin Tsarki Yana cewa: “Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.” (K:15:95). Kan tafsirin wannan aya Ibn Sa’ad (Rahimahullah) ya ce: “Hakika Allah Ya aikata haka, babu wanda ya bayyana isgili ga Manzon Allah (SAW) da abin da ya zo da shi face Allah Ya hallaka shi, Ya kashe shi mugun kisa.” Sannan Dabarani a cikin Al-Ausad da Baihaki da Abu Nu’aim su biyun a cikin Ad-Dala’il da Ibn Madawiyya da sanadi mai kyau da Ad-Diya’u a cikin Almukhtarat sun ruwaito daga Ibn Abbas (RA) kan fadinSa Madaukaki: “Lallai ne Mu, Mun isar maka daga masu isgili.” Ya ce: “Masu isgilin su ne Walid bin Al-Mugira da Al-Aswad bin Abdu Yagusa da Al-Aswad bin Mudallib da Alharis bin Andalus Sahmiy da Al-As bin Wa’il…”
Karashen Hadisin ya nuna dukkansu Allah Ya hallaka su daidai da daidai da cututtuka daban-daban, wadansu daga cikinsu ma ba a garuruwansu ba.
To sai dai ya ku bayin Allah! Mene ne matsayinmu a yau? Wajibi ne mu tambayi kawunanmu: Shin muna son Manzon Allah (SAW) so na gaskiya, ko kuwa muna fada ne kawai a baki? Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Dayanku ba ya zama mai imani, har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifinsa da dansa da dukan mutane.” Kuma Umar bin Khaddabi (RA) ya taba cewa: “Ya Manzon Allah! Wallahi kai ne mafi soyuwa a gare ni baya ga raina. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Ba haka ya kamata ba. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, (ba za ka zamo mai imani ba) sai na kasance mafi soyuwa a wurinka daga ranka.” Sai Umar ya ce: “Lallai kai a yanzu wallahi kai ne mafi soyuwa a wurina daga raina. Sai Annabi (SAW) ya ce: “Yanzu ne (ka yi imani) ya Umar.”
Mu tuna Abubakar Siddik (RA) wanda ya rika kukan farin ciki lokacin da ya ji cewa shi ne abokin tafiyar Manzon Allah (SAW) a yayin hijirarsa. A kan hanyarsu ta hijira idan ya tuna za a kawo hari ta gaba, sai ya koma gabansa (SAW), idan kuma ya tuna za a biyo su ta baya, sai ya koma bayan Manzon Allah (SAW), har suka isa Madina yana mai fansar Annabi (SAW) da ransa!
Sannan mu tuna Nusaiba bintu Ka’ab Al-Maziniyya Ummu Ammara (RA), mace ce da ta dauki takobi tana kare Manzon Allah (SAW) a lokacin da maza suka guje daga gare shi. Ya taba ce mata: “Tambaye ni abin da kike so Ya Ummu Ammara.” Sai ta ce: “Ina rokonka kasancewa makwasbciyarka a Aljanna da sonka a duniya da sonka a Lahira.”
Sannan da aka kammala yakin Uhudu sojojin Annabi (SAW) sun wuce ta wurin wata mace a hanyarsu ta dawowa Madina alhali an kashe mijinta da dan uwanta da mahaifinta, amma da aka yi mata ta’aziyya sai ta ce: “Me ya samu Annabi (SAW)? Suka ce ba komai sai alheri ya Ummi wane! Yana nan lafiya bisa godiyar Allah kamar yadda kike so.” Sai ta ce: “Ku nuna min shi in gan shi. Sai aka yi mata ishara zuwa gare shi, a lokacin da ta gan shi sai ta ce: “Duk wata musiba a bayanka (in ba ta shafe ka ba), karama ce!”
Kuma lokacin da Kuraishawa suka aika Urwatu bin Mas’ud As-Sakafiy (RA) yana mushiriki a lokacin Sulhun Hudaibiyya, da ya ga irin son da sahabbai suke yi masa (SAW) ya koma zuwa ga Kuraishawan ya ce musu: “Ya ku mutanena! Wallahi hakika na bakunci sarakuna na bakunci Kaisar da Kisra da Najjashi, wallahi ban ga wani sarki ko shugaba daya da mutanensa suke girmama shi kamar yadda sahabban Muhammad suke yi ga Muhammadu ba. Wallahi bai tofar da kakinsa face ya fada a tafin hannun wani namiji daga cikinsu ya shafe shi a fuskarsa da jikinsa. Idan ya umarce su, sai su yi gaggawar aiki da umarnin. Idan yana alwala kamar za su yi fada kan neman ruwan alwalarsa. Idan yana magana sukan yi shiru, kuma ba su iya daga ido su kalle shi saboda girmamawa gare shi.”
Wannan shi ne son sahabbai ga Manzon Allah (SAW). Shin muna son Manzon Allah (SAW) ko dai al’amarin ya tsaya ne a da’awar baka kawai? Shin muna girmama shi? Shin muna yada sunnarsa? Shin muna ladabtuwa da ladubbansa? Shin muna koyi da shiriyarsa? “Lallai Mu, Mun aike ka, kana mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma mai gargadi. Domin ku yi imani da Allah da ManzonSa, kuma ku girmama shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) safiya da maraice.” (K:48:8-9).
Allah Ya yi min albarka da ku cikin bin Alkur’ani Mai girma. Kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima. Ina fadin wannan magana tawa, ina neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai Shi ne Mai gafara Mai jin kai.