✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani abin kunya a Majalisar ministoci

Jabun shaidar kamala karatu ba bakon al’amari b ane a ko’ina cikin duniya. A hakikanin gaskiya ma har a kasashen da suka ci gaba, wadand…

Jabun shaidar kamala karatu ba bakon al’amari b ane a ko’ina cikin duniya. A hakikanin gaskiya ma har a kasashen da suka ci gaba, wadand asuka hada da Amurka da Jamus ana samun irin wannan, shekara biyu da suka wuce aka tursasa wani minista ya sauka daga mukaminsa, saboda ya tsakuro wasu bayanai a cikin kundin digirin digirgir din wani, ba tare da ya yi nuni da inda ya dauko ba. Sai dai irin wannan hark ace d ake samun ci gaba a Najeriya.
Fafutikar da ake yi wajen samun mukaman gwamnati a Najeriya, yana da matukar tayar da hankali, ta yadda ake bi kowace irin hanya, mai kyau ko mara kyau, don samun fifiko, a dara wanda ake gasa da shi. Ta yiwu wannan ce ta sanya ake samun jimurda wajen tantance wanda ya cancanci rike mukamin hukuma, ta yadda ake saba wa ka’ida idan wanda za a tantance zai iya biyan bukatun son ran wasu.
Labarai sun bazu a game Minista a Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, wadda ke kula da Safarar Jiragen Sama, Misis Stella Odua, wadda akce tana da matsala shaidun karatunta, kodayake ba bakon abu ba ne, amma al’amarin abin takaici ne. Rahotanni sun bayyana cewa Kwalejin St. Paul Lawrencebille birginia da ke kasar Amurka, duk da  yake Misis Oduah tsohuwar dalibar makarantar ce, ta yi digirin farko ne kawai a fannin lissafin shige da ficen kudi, amma makarantar ba taba bai wa wani digiri na biyu ba, a tsawon tarihinta na shekara 125. Wani ikrarin da Oduah ta yi na samun digirin girmamawa daga Jami’ar Pacific Christian an jefa wa lamarin shakku, domin Sashen kula da harkokin ilimi na Gwamnatin Amurka, ya yi nuni da cewa, babu wannan makaranta a Jihar Kalifoniya. Digirin girmamawa na da saukin samu a wannan zamanin, don ko ta kafar sadarwar intanet mutum zai iya samu, don haka wannan al’amari yake matukar rudarwa, kan yadda mutum zai yi jabunsa!
Lallai akwai buktar duk wadanda suke fafutikar ganin an nada su mukaman gwamnati, sun samu cikakkiyar tantancewa ta nagartar halayensu. Ta tabbata cewa Hukumomin Gwamnati ba su cika bibiyar nagartar  takardun makaranta yadda ya dace. Mafi karancin abin da za a tantance kafin a tabbatar da cancantar wanda za a nada mukami, don tabbatar da makarantar da ya halarta, akwaita, kuma tana gudanar da kwasa-kwasai irin wadanda aka nuna a shaidar karatun.
Duk da cewa ba za a dauki uzurin gwamnati a kan irin wannan  sakacin ba, su ma jami’o’i da ke bayar da shaidun kamala karatu suna da nasu laifin. Gazawar da ake nunawa wajen tabbatar da ingancin shaidun kamala karatu ga masu neman rike mukaman gwamnati, ya yi kamari ta yadda har jabun  Farfesoshi ake samu a jami’o’in. Akwai likitocin bogi, wadanda suka yi badda kama, suna ta aiki tsawon shekaru; ga lauyoyin bogi, wadanda ke hanzari fitowa gaban alkali tun kafin a kirawo su; akwai ’yan jaridar bogi, wadanda ke bin son ran jami’an gwamnati da ’yan siyasa., tare da sauran masu ikrarin shaidu kan al’amuran da suka shafi kamfanoni masu zaman kansu da ofisoshin gwamnati.
Akwai dalilai da dama da suka sanya ake yin jabun shaidun karatu, al’amarin da ya zama rowan dare game duniya, har aka kasa ganowa a Najeriya. Lalacewar ayyukan gidan waya, su suka sanya aikewa da samun amsar tantance ingancin muhimman takardu yake da wuya. Abu na biyu, mafi yawan jami’o’i ba su da managarcin tsari, wajen adana bayanan tsofaffin dalibai. Abu na uku, Najeriya ta zama kasar da ake bai wa shaidar karatu fifikon muhimmanci kan kwarewar aiki. Bukatar da kawai ake so ga mai neman mukami, shi ne ya aike da kwafen takardun makarantarsa, maimakon a aike wa makarantun da ya halarta, don su tabbatar da cewa wadannn takardu ba an same su ta haramtacciyar hanya ba.
Ya kamata gwamnati da sauran masu bayar da ayyukan yi su rika bin kadin takardun karatu, ta hanyar amfani da dabarun da ake bi a mafi yawan kasashe, inda mai neman mukami ke cika takardar bayanai, ya bayyana makarantun da ya halarta da irin kwarewarsa, ta yadda za a tantance ingancinsu kafin a bai w amutum mukamin. Hukumar Kula da Jami’o’i, ya kamata ta yi rumbun bayanai a kan daukacin ‘’yan Najeriya da suka kamala karatunsu a jami’o’in, sannan a samar da cibiyar tantancewa a duk lokacin da bukata ta taso. Muhimmancin da ke tattare da tantance ingancin shaidun kamala karatu ga masu rike da mukaman gwamnati, wadanda suka hada da jami’an asiri na “SS”, don a tabbatar da cewa wadanda ke wakiltar Gwamnatin Tarayya, sun zama mutane nagari, wadanda halayensu ke nuni da kyawawan dabi’u. Yadda ake yawan gano jabun takardun kamala karatu a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati, na nuni da cewa hukumomi ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ko kuma suna karya ka’ida don kace wa abin da suka sani. Wannan cutar da kasa ne.