✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane ne Mohammad Hasan Akhund, sabon Shugaban Afghanistan?

Ana yi masa kallon ba ya cikin mutanen da aka fi jin muryoyinsu a kungiyar.

Da yammaci ranar Talata ne kungiyar Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar Afghanistan wacce za ta kasance karkashin jagorancin Mullah Mohammad Hasan Akhund, a matsayin sabon Shugaban Kasa.

Kungiyar ta kuman nada Abdul Ghani Baradar a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa, yayin da Sirajuddin Haqqani zai kasance sabon Ministan Cikin Gida, kamar yadda kakakin kungiyar, Zabihullah Mujahid ya sanar yayin wani taron manema labarai a birnin Kabul.

Bugu da kari, Taliban ta kuma nada, Mullah Mohammad Yaqoob, da ga Mullah Omar wanda ya kirkireta a matsayin sabon Ministan Tsaro.

Wane ne sabon Shugaban Afghanistan?

Mullah Mohammad Hasan Akhund shi ne shugaban sashen da ya fi kowanne karfin fada-a-ji na kungiyar wato ‘Rehbari Shura’, wanda yake kamar matsayin Majalisar Zartarwar kungiyar da ke da wuka da nama wajen tafiyar da lamuranta, bisa amincewar jagoran Taliban.

Rahotanni sun ce jagoran kungiyar Mullah Hebatullah da kansa ne ya bayar da sunan sabon Shugaban don ya jagoranci sabuwar gwamnatin.

Mullah Hassan dai dan asalin Kandahar ne, garin da nan ne ake yi wa kallon cibiyar Taliban kuma yana daya daga cikin wadanda suka kirkiri kungiyar.

Ya jagoranci majalisar Rehbari Shura na kusan tsawon shekara 20, kuma ana kallonsa a matsayin wanda ke da kusanci matuka da Mullah Hebatullah.

A tsakanin shekarun 1996 zuwa 2001, ya kasance Ministan Harkokin Waje da kuma Mataimakin Firaministan Afghanistan lokacin mulkin Taliban.

Sai dai ana yi masa kallon cewa ba ya daya daga cikin wadanda aka fi jin muryoyinsu a kungiyar ko suke da karfin fada-a-ji a cikinta.

Kazalika, a watan Maris na shekarar 2001, shi ne ya jagoranci lalata wajen ibadar mabiya addinin Buda da aka fi sani da Bamiyan, kuma har yanzu sunansa na cikin jerin wadanda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin ’yan ta’adda.

“Mullah Akhund ya yi aiki na kusan shekara 20 a matsayin jagoran Rahbari Shura. Ya fi siffantuwa da mutum mai riko da addini fiye da aikin soja, kuma ya yi suna wajen riko da addini,” inji jagoran Taliban, Hibatullah Akhundzada.