Jagororin Arewacin Najeriya sun ce dan takarar da zai iya magance matsalar tsaro da sauran kalubale da ke addabar yankinsu kadai za su goyi baya a zaben shugaban kasa na 2023.
Shguabanin daga jihohi yankin 19 da Birnin Tarayya sun bayyana matsayin nasu ne a taron kwana biyu da kungiyar Sabuwar Ajandar Arewa (ANA) ta shiyra a Abuja.
- Har Yanzu Shekarau ne dan takarar NNPP a Kano ta Tsakiya —INEC
- ’Yan fashi masu amfani da tsafin barci sun shiga hannu a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Shin Yakin Neman Zabe A Kafafen Sada Zumunta Zai Yi Tasiri?
Sun bayyana cewa matsalar tsaro, rabuwar kai da zama koma baya da sauran matsaloli sun haka yankin Arewacin Najeriya samun ci gaban da ya kamata.
Sun kuma nun takaicinsu bisa abin da suka kira gazawar shugabanin yankin wajen daukar matakai da suka dace wajen yi wa tufkar hanci.
A jawabinsa, Sakare-Janar na Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF), Murtala Aliyu, ya ce wajibi ne yankin “ya shi da gaske wajen tattaunawa da shugabannin siyasar Najeriya domin tabbatar da cigaban yankinmu ba tare da bata lokaci ba.”
A nasa jawabin, Daraktan Gidan Tarihi na Arewa, Dokta Shuaibu Aliyu, ya bayyana cewa har yanzu Arewa ne yankin da ke zaman kashin bayan hadin kan Najeriya.
Sanata Ahmad Moallahyidi, wanda shi ne ya kira taron, ya ce a matsayin Arewa mai fadin kasa da ya kai kadada milyan 98.3, wanda daga ciki ake iya noma kadada miliyan 82, ba Najeriya kadai yankin ke ciyarwa ba, har da daukacin yankin Saharar Afirka.
Don haka ya jaddada muhimmacin magance matsalolin yankin domin amfanin al’umma.