✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ake zargi da kisan Hanifa ya yi mi’ara koma baya

Abdulmalki ya ce sam ba shi ya kashe ta ba.

Shari’ar da ake yi kan zargin kisan Hanifa, daliba mai shekara biyar a Kano ta dauki sabon salo, bayan da wanda ake zargi da kisan nata, Abdulmalik Tanko ya ce sam ba shi ya kashe ta ba.

A yayin zaman Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Naabba ranar Litinin, Abdulmalik, wanda kuma shi ne malamin makarantar su Hanifa ta Noble Kids ya musanta hannu a kashe ta.

Hakan na zuwa ne bayan a baya wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya kashe ta, kwanaki 47 bayan ya yi garkuwa da ita, inda dubunsa ta cika lokacin da yake kokarin daukar kudin fansarta da aka kai masa.

Sai dai a zaman kotun da ya gudana ranar Litinin, wanda ake zargin da kisan Hanifa Abubakar, wato Abdulmalik Tanko, ya musanta zargin kisan nata.

Tun da farko masu gabatar da kara karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, sun gabatar da takardar caji ga kotu inda aka karanta wa wadanda ake zargi.

Wadanda ake kara sun amsa aikata laifin tuhuma ta farko na hadin baki wajen yin garkuwa da Hanifa, laifin da ya saba da sashe na 97 a Kundin Shari’a na Penal Code.

Sai dai kuma sun musanta aikata tuhuma hudu da suka hada da ta yunkurin garkuwa da Hanifa a karo na farko da neman kudin fansa daga iyayenta da tuhumar kisanta da kuma ta binne ta cikin makarantar North West da ke Tudun Murtala, laifukan da suka saba da sassa na 95 da 221 da 277 a Kundin Sharia na Penal Code.

Masu gabatar da kara sun nemi kotu ta ba su izinin gabatar da shaidunsu a gabanta a zama na gaba.

Sai dai lauyan wadanda ake zargi, Barista Labaran Usman, ya nemi kotu da ta ba su dukkanin takardun shari’ar don yin nazari  kan shari’ar.

“Muna neman kotu ta ba mu takardun shari’ar don mu fahimceta, wanda hakan shi zai ba mu dama a gudanar da shari’ar cikin sauri,” inji su.

Alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya sanya ranakun biyu da uku ga watan Maris din 2022 don sauraren shaidun masu gabatar da kara.

Ya kuma yi umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali har zuwa lokacin.

%d bloggers like this: