✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda aka haifar masa ’ya’ya biyar lokaci daya ya ce a taimaka masa

Mutumin da matarsa ta haifa masa ’ya’ya biyar a lokaci guda a karshen makon jiya, a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Lakwaja fadar Jihar…

Mutumin da matarsa ta haifa masa ’ya’ya biyar a lokaci guda a karshen makon jiya, a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Lakwaja fadar Jihar Kogi, Mista James Okeigbo ya bukaci gwamnati da  jama’a su tallafa masa.

Bincike ya nuna  ma’auratan sun shafe shekara 18 ba tare da samun haihuwa ba sai a wannan karon.  Mista James ya ce yana neman tallafi daga wajen gwamnati da al’umma ne domin ci gaba da daukar nauyin wadannan jarirai.

Matar ta haifi jarirai maza uku ne da mata biyu ta hanyar dasa mata kwayoyin hallita.

James mai kimanin shekara 47 ya fito ne daga Jihar Abiya, kuma ya jinjina wa matarsa saboda hakuri da kuma juriyar da ta nuna a yayin haihuwar jariran biyar.

Kakakin Majalisar Jihar Mista, Matthew Kolawale, ya kai ziyara asibitin inda ya mika gudunmawa domin tallafa wa iyalan.

Wata jami’ar asibitin, Misis Adeosun ta ce wannan haihuwar ’yan biyar a lokaci daya, wani al’amari ne daga Allah kuma wannan shi ne karo na farko da aka taba haifar ’ya’ya biyar a lokaci daya a asibitin.