✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakilan Aminiya sun tsallake rijiya da baya a Kano

“...na ɗauka sai ɓata-garin sun kashe abokin aikin nawa saboda yadda na ga suna ƙoƙarin burma masa wuƙa bayan ya faɗi shame-shame a ƙasa.”

Wasu wakilan Kamfanin Media Trust Group, mamallakan jaridun Aminiya, Daily Trust, Trust TV da Trust Radio, sun tsallake rijiya da baya a wani rikici da ya rutsa da su a Filin Idi da ke Kofar Mata a Jihar Kano.

Lamarin dai ya faru ne yayin da ’yan kasuwa da ke kasa kaya a bisa tebura da shagunan wucin gadi a jikin katangar filin Idin suka shiga zanga-zangar adawa da tashin su daga wurin da gwamnatin Kano ta yi.

Aminiya ta ruwaito cewa, ɓacin rana ya rutsa da wakilan bata ne a yayin da ɗaya daga cikinsu ya taho a guje yana tsala ihun ankarar da abokan aikinsa da su ranta a na kare su nemi mafaka.

“Ina cikin tambayar ko ina Khalid [Aminiya] ya shiga, sai kawai na jiyo ihunsa yana ce min Abdul ka gudu sai can ga shi ya taho a sukwane.

“Da muka fahimci cewa ɓata-gari ne suka biyo Khalid ɗauke da makamai, nan da nan muka bi sahunsa muka arce.

“Muna tsakar gudu wata mota ta buge ɗaya daga cikinmu [Abdul] da ke ɗaukar hotuna da bidiyo, inda a nan ɓata-garin suka zagaye shi bayan ya faɗi ƙasa wanwar.

“Har ɗaya daga cikin ɓata-garin ya zaro wuƙa mai tsini zai soka wa Abdul, sai wani ya tari hanzarinsa sannan ya ƙyale shi.”

A nasa ɓangaren, wakilin Trust TV, Idris Jibril, ya ce, “gaskiya wannan lamari ya tayar min da hankali don na ɗauka sai ɓata-garin sun kashe abokin aikin nawa saboda yadda na ga suna ƙoƙarin burma masa wuƙa bayan ya faɗi shame-shame a ƙasa.

“Ina ganin haka na gaggauta ɓoye makirifon da ke hannuna a cikin aljihu don kar na ɗauki hankalinsu su dawo kaina,” in ji shi.