Duk wanda ya budi ido a zamanin nan ya san yadda al’ummarmu ta mayar da wannan bakar al’ada ta Turawan yamma ado,watau fati(party).Yadda za a gane cewa abin ya zama hantsi leka gidan kowa kuwa shi ne idan aka duba katin gayyatar bukukuwa za a ga cike yake da shagulgulan fatiirin su‘dinner,launching,sitting’wanda yawanciakan hada maza da mata. Kuma akawai na sharholiyar murnar zagayowar ranar haihuwa(birthday party) da na gama makaranta da na barka da sallah da dai sauransu.
Ganin mata ne abin ya fi yi wa illa,ya sa nake son jawo hankalinsu da iyayenmu domin su yi hannun riga da abin don kada ya zama da-na-sani wadda keya ce kuma daga baya take. Rashin kunya da karyar da ake yi saboda fati suna da yawa;ana samun ‘yan mata har da matan aure suna yin shiga kamar suna tsirara ko kuma su fita da hijabi amma da sun je sai su cire su yafa dan gyale taya-ni-gantali.Ba ma nan gizo yake sakar ba sai an je wurin yin,domin ana gabatar da tsarin ‘pick & obey’wato za a rubuta lambobi a cikin ‘yan kananan takardu a rarraba wa mutane,sai duk wanda aka kira lambarsa ya fito, mai gabatarwa zai karanta umarnin lambar don wanda ya dauko ya aiwatar,idan kuwa ya kasa za a ci shi ta tara.Ko kawai haka nan a fada da baki a yi rawa har irin ta Indiyawa da sumbatar juna,kai uwa uba ma har da shafe-shafen jikin juna .Ga shi manzon Allah(S.A.W) ya ce”Ya fi alheri ga dayanku a buga masa allura ta bakin karfe a cikin kansa da ya shafi hannun macen da ba ta halarta gare shi ba”.Dabarani ya ruwaito shi kuma Albani ya inganta shi.
Wannan ne yake sanyawa ake ganin dokin samari da ‘yan mata ya bayyana na gudanar da fati,don ‘yan mata na haduwa da samari kala-kala a wurin domin duk munin mace wani na iya yi mata magana a wurin,wannan gamin-gambizar ce ke sa yin zina a saukake domin dama duk yawanci mara sa aure ne,ga kuma mata sun fitowa kamar suna tsirara.
Wasu abubuwa masu ban tsoro da saka firgici da kawo matsaloli a cikin rayuwar fati su ne ana yi ne da daddare har ana fara
wani tun daga 12 na dare zuwa Asuba (till dawn),wani karin haushi ma shi ne har a cikin daji ake gabatar da wannan ta’asar. Sai a je da motoci a kunna fitilunsu,wanda abu ne mai sauki a yi gamo da aljanu idan ba a yi sa’a ba, ko kuma a hadu da bata-gari su yi wa wata fyade.Ko mazan da suka shirya fatin su zuba wani abu mai bugarwa su bai wa matan su yi lalata da su(don an yi haka a Katsina).
Za mu ci gaba!