✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wakar ‘Maryam Mariya Maryam’ ce ta fito da ni – Mamman Barka

Mamman Barka shahararren mawakin gargajiya ne a Jamhuriyar Nijar. Wakokinsa sun dade suna nishadantarwa da ilimantar da al’umma a kasarsa ta Nijar da Najeriya da…

Mamman Barka shahararren mawakin gargajiya ne a Jamhuriyar Nijar. Wakokinsa sun dade suna nishadantarwa da ilimantar da al’umma a kasarsa ta Nijar da Najeriya da sauran kasashen Afrika da ma sassan duniya daban-daban. A makon da ya gabata ne wakilinmu ya yi kicibus da shi a yayin taron tunawa da margayi Farfesa Hambali Jinju a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. Mawakin ya yi gamsasshen bayani game da rayuwarsa, wakarsa da sauran al’amura da suka shafe shi. Ga yadda ganawar ta kasance:

Wane ne Mamman Barka?
An haife ni ne a shekarar 1958, a Taskir, wani kauye da ke cikin Jihar Damagaran, Jamhuriyar Nijar. Iyayena sun kasance ’yan kabilar Tibawa. Mutanen daji ne, masu noma da kiwon dabbobi. Muna kiwon rakuma a cikin daji. Ba mu da shanu, amma muna da dangantaka da Fulani da sauransu. Na yi karantun zamani, na yi firamare kuma na yi sakandare a makarantun gwamnati, sannan sai aka tura mu muka zama malaman makaranta.
Na samu kimanin shekara biyu zuwa uku ina koyarwa a karkararmu, wato a cikin daji. A lokacin nan ne na ga wani yaro yana kada gurmi. Na ga yaron ya iya kidan gurmin nan sosai, don haka sai na kira shi, na ce ya koya mani. Zan iya tunawa, a shekarar 1981 ne na gamu da yaron nan. Ya koya mani kuwa na tsawon shekara daya, daga nan muka rabu da shi. Daga nan ne aka kai ni wani kauye daban, inda a nan na tuno da wani makadin gurmi da ya shahara a duniya, wato Haruna Uji na Najeriya. Na je na sayi kasa-kasensa ina saurare, na rubuce dukkan wakokinsa, na rika yin irin kidansa kuma ina rera wakokinsa. Daga wadannan wakoki na Haruna Uji, sai ni ma na kirkiro nawa salon kidan na daban. Na shigo da wakar ‘Maryam Mariya Maryam’ da wakar ‘Kyar-Kyar-Di-Kyar-Kyar’ da sauran wakoki. Na samu na shirya faya-fayai guda tara na irin wadannan wakoki na gurmi. Faya-fayen nan sun kunshi wakoki sama da guda dari daya.
Faifain wakokina na farko yana da wakoki goma sha bakwai, shi ma na biyu, ya kunshi wakoki goma sha bakwai. Ka ga idan aka tara wakokin faya-fayai biyu ma kawai, za a samu wakoki talatin da hudu. Ka ga wakoki talatin da hudu, watakila wakoki ne da wani karamin mawaki zai yi su a tsawon rayuwarsa duka.
Wace ce Maryam Mariya Maryam?
Mariya Maryam wata yarinya ce. Lokacin da na san ta tana karama a nan birnin Yamai, a nan take. Lokacin da na san ta, na sauka ne a gidansu, domin ita kanwa ce ga abokina. A lokacin da na je gidansu, tana ’yar shekara goma zuwa sha daya da haihuwa. Duk mutanen gidan nasu, yaren Zabarmanci suke yi, ni kuwa ban iya ba a lokacin. Ita kuma a lokacin ta iya Hausa, amma kadan. Ban sani ba ko tsakanin yara kawayenta ta koya? Kamar alal misali idan tana so ta ce ‘jiya da daddare’ sai ta ce ‘wancan duhu da ya wuce.’
Haka nan muka yi zama da ita, yarainyar nan tana karama. Ni na zo nan Yamai a matsayin hutun makaranta ne, domin ba aiki nake ba. A lokacin da nake hutun nan, kullum akan bar ni gidan ni kadai kamar misalin karfe takwas na safe, sai dai yara. Ita kuma kudin da ake ba ta domin karin kumallo sai ta je ta sayo waina (masa) ko wani abin karin safe, sai ta kawo ta aje mani daidai kaina, ina kwance ina barci. Idan na tashi sai dai in ji abinci yana kanshi a kusa da ni, kawai sai dai in dauka, in bude in ci. Haka nan take yi mani, wani lokaci haka sai ta yi sati guda tana tara ’yan kudi, a karshen satin sai ta kawo dala arba’in ko dala sittin, ta ce mani: ‘amshi ka je silima ka shiga.’
Wannan yarinyar ita ce na yi wa wakar nan. kauna ce kawai ta hada mu da ita amma ba batun soyayya ta saurayi da budurwa ba, kauna ce kawai, kauna ce ta yarinya karama. Daga baya dai ta girma, ta yi aure. Amma abin da na sani kuma na tabbatar shi ne, wakar wannan yarinya ita ce ta fito da ni a duniyar waka.
Ko wannan zumunci tsakaninka da ita ya dore kuwa?
Zumunci ya dore kuwa saboda gidansu, wato abokin nawa ya rasu amma ni ina tare da zumuncin iyalinsa tare da ’yan uwansa har yanzu, muna zumunci da juna.
Ina batun aikinka na farko, wato koyarwa, ka bari ko har yanzu kana yi?
Ban jima ba in akoyarwa, shekara bakwai na yi ina koyarwa, daga baya sai aka mayar da ni aiki a Hukumar Wasanni Da Al’adun Gargajiya. Yanzu a can nake aiki, kodayake na kusa yin ritaya nan gaba kadan, shekara biyar masu zuwa. Kodayake ka san mu mawaka ba mu yin ritaya, domin ko mun bar aikin gwamnati, za mu ci gaba da sana’armu a kullum.
Game da sana’arka ta waka, me ka samu a sanadiyyarta, wanda ba za ka mance da shi ba?
Na samu suna gabas da yamma, gusun da arewa ko’ina cikin duniya, na ga duniya. Ina zuwa kasashen Turai, Amurka da sauransu, ko’ina da kasashen Afirika. Na san manyan mutane, haka su ma sun san ni. Na zauna tare da shugabanni kasa na Turawa da na Afirika da na Asiya. Ina alfahari da wannan, amma dai ni mutum ne wanda zan ce ba wata dukiya ke gare ni ba amma dai ina da suna kuma ina da arziki na cikin zuciya (wadatar zuci).
Mamman Barka, maganar iyali fa?
Kafin ka yi mani tambayar iyali, na so ka yi mani wata tambaya game da wata yarinya a Najeriya, wadda ake kira da suna Sa’adatu. A cikin rayuwata, lokacin da na yi samartaka, babu wata yarinya wacce daga wata kasa ta taso ta zo, ta ce tana so na sai ita. Ta taso tun daga Kano ta zo wajena alhali ba ta taba zuwa Nijar ba sai lokacin. Na yi mata waka a faifaina na bakwai, wakar ‘Inde-Ker-Ker-Di-Ker-Ker Sa’adatu ’Yar Budurwa, Sa’adau ’Yar Kanawa.’ Zancen iyali, ina da mata daya da ’ya’ya goma. Ba mu yi aure da ita ba, tuni ta yi aurenta amma mun zama ’yan uwa.
A cikin ’ya’yanka ko akwai wanda ya dauko gadonka na waka?
Ni da kaina ban gada ba, domin tun farko ni waka sha’awa ce na dauke ta. Ba zan tilasta wa wani dana cewa sai ya yi ba. Na koya masu kida da waka, sun dan yi makaranta. Guda ya yi Fiyano, daya kuma ya yi Jita, guda ya yi Jambe, sun samu shekara biyu suna koyo, daga baya sai na ga sun zubar da wannan kayan kida, kowa ya shiga sha’anin neman ilimi, yana karatunsa.
Daga karshe, mene burinka a rayuwa?
Yanzu ina nan ina rubuta littattafai. Na rubuta littafina na farko, wanda ke bayyana balaguron da muka yi a cikin kasashen Turai, na bi tafiyar rana-rana na rubuce abin da ya gudana tsawon kwana arba’in da biyar. Akwai kuma littafin da na rubuta, wanda ya kunshi tarihin manya-manyan makada da mawaka na zamani na nan Nijar, tun daga 1960 zuwa yanzu. Littafina na uku kuwa ya kunshi kayan kida da kuma irin kade-kade na gargajiya na kasar Nijar. Littafina na hudu wanda ban kammala ba shi ne, wanda ya kunshi ainahin masaniya game da yaren Tibawa da yanayin rayuwarsu. Don haka a burina, ina son rubuta littattafai domin in bar wa na baya tarihi. Ina son a rayuwata ta duniya, kafin Allah Ya dauki raina, a ce na kawo wata gudunmowa ta musamman wajen bunkasa addinin Musulunci. Ina son in ga cewa an gina wa matasa makarantu na addinin Musulunci. Ina da burin in ga na gina manya-manyan masallatai na Juma’a, domin kuwa idan addini ya ginu bisa ilimi, ya yi karfi, to lallai kam rayuwa za ta saukaka ga al’umma, wasu rikice-rikice cikin al’umma za su kau ko kuma su rage sosai.