Ga wata waka mai taken ‘Wakar Ebola’ da fasihi A Y Husain (AYAH) ya yi mana guzurinta. A cikin wakar ya bayyana alamomin da ke nuna kamuwa da cutar Ebola, ya gargadi mutane cewa gishiri da namijin goro ba sa magance cutar, sannan ya bukaci a rika tsabta da kuma addu’a domin neman kariya:
Amshi:
Cutar ga da tayyo razani,
Rabbana kare mu da hanzari,
Nahiyar mu kasa Najeriya,
Ga Ebola tana son kada mu.
Baituka:
1 Rabbi Sarkin dukkan duniya,
Sunanka na faro kafiya,
Kare ni Ilahu da lafiya.
Zan yi bayani kar nai tirjiya.
2 Nai jugum na kasa katabus,
Ga jikina ya mutu yai murus,
Labari a kunnena yai fus-fus,
Wai Ebola ta shigo Najeriya.
3. Dole in yi salati ga annabi,
Gwarzona ya al-mahabubi,
Tabi’ai da dukkan sahibi,
Sun wafati sun bar duniya.
4.’Yan uwa mu gyara tunani,
Zuciya tamu kar tai rauni,
Kan Ebola da tazzama hauni,
Na gani da yawa mun karaya.
5. Zan bayani to fa ku marmatso,
Don fahimta taku yi za na so,
Yadda ke yado har ta karaso,
Zan bayani a jerin kafiya.
6.Ba a daukar Ebola a iska,
Numfashi ko ba a farraka,
Sam Ebola fa ba ta biyo ka,
Kar tsan kyamar ikiwaniya.
7. Amma mu guji hada jiki,
Don Ebola takan bi jiki daki,
Mu kiyaye in mun kai tsaki,
Nan da nan za tai makiya.
8. Bayyanar cutar ga Ebola,
Daga ka kamu taka kula,
Duk alamu nata su bulla,
Bai wuce kwana ishiriniya.
9.Alamomin har da gudawa,
Zazzabi mai zafi ko kuwa,
Yin amai ba kaukautawa,
Duk gababincir rasa lafiya.
10.Ciwon kai ya zo marar dadi,
Har abinci ya zam babu gardi,
Ciwo na ciki ya yi rudi,
Makaki a makoshi da jijiya.
11. Babu mamaki a ga kurji,
Jan ido ko zafi na kirji,
Numfashi da kyar tari da ji,
Ya zamo da kyar ke hadiya.
12. Bayan gida a ciki da jini,
Ko tari in kai za a ga jini,
Majina in ka fyato sai jini,
Da alama Ebola tana biya.
13. Gishiri fa ba ya magani,
Ga Ebola mun gane tuntuni,
Likitoci nata na gani,
Kar mu kai kanmu ga taraliya.
14. Namijin goro mu guje shi,
Ko da dai na san an so shi,
Amma ku sani fa yawan shi,
Na illa kar mu yi tankiya.
15. Rabbi sarki ga rokonmu,
Kare mu da dukkan hammu,
Kar Ebola ta ma shafe mu,
Mu gare Ka muke yin rokiya.
16.’Yan uwa na ce don Allah,
Mu natsu mu kauce dalala,
Jita-jita kar da mu kula,
Addu’a mui ta neman kariya.
17. Sunan mai wakar AYAH,
Jostis Aleeyou na Zariya,
Jikan Katsinawa ba riya,
Unguwa ta Mu’azu Kaduniya.
A Y Husain AYAH ya rubuto daga Unguwan Mu’azu Kaduna