✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wajibi ne NNPC ya samar wa gwamnati kudi – Hukumar RMAFAC

Hukumar Tarawa da Raba Arzikin kasa, (RMAFAC) ta ce bisa bayanan da ke hannuta, kamfanin man fetur na kasar wato NNPC ya ki sanya kudi…

Hukumar Tarawa da Raba Arzikin kasa, (RMAFAC) ta ce bisa bayanan da ke hannuta, kamfanin man fetur na kasar wato NNPC ya ki sanya kudi da yawansu ya kai tiriliyan biyar, a cikin asusun gwamnati.
Hukumar RMAFAC ta ce a tsawon shekara biyar, NNPC bai zuba kudin a baitil malin gwamnati ba, kamar yadda BBC ya bayyana.
A saboda haka, hukumar ta ce dole ne kamfanin   ya mayar da kudin domin haka doka ta tanada.
Wannan dai na zuwa ne kimanin mako guda da ofishin babban mai binciken kudi na gwamnati, ya fitar da rahoton da ke zargin cewa a shekarar 2014, kamfanin ya ki zuba dala biliyan 16 a asusun gwamnati. Sai dai kamfanin ya musanta zargin.