✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wai da gaske lemon kwalba na Schweppes yana maganin zazzabin cizon sauro?

  Wai shin lemon nan na kwalba na Schweppes magani ne na zazzabin cizon sauro? Domin kamar na taba jin hakan. Idan ma na sha…

 

Wai shin lemon nan na kwalba na Schweppes magani ne na zazzabin cizon sauro? Domin kamar na taba jin hakan. Idan ma na sha shi na kan ji kaikayi a jikina kamar na sha maganin zazzabin?

Daga Zainab A. Kebbi

Amsa: Lemon Schweppes na asali wato tonic water an hada shi ne domin kare turawan mulkin mallaka na Afirka da Indiya daga ciwon zazzabin cizon sauro. Shi tonic water wani ruwan magani ne da ke dauke da ganyen bishiyar cinchona mai sinadarin kuinine, wannan dai sinadari da ake sa wa a maganin zazzabin cizon sauro na chlorokuine. Za a ji shi dandanonsa da daci sosai saboda wannan sinadari.

To su Turawan mulkin yadda suka fara hada ruwan tonic shi ne sukan zuba garin kuinine ne a lemukansu da giyarsu domin kawai dandanon dacin, sai daga baya ne suka gano yana iya kiyaye mai sha daga zazzabin cizon sauro.

Sai da wannan ruwa yai suna a wancan lokaci aka fara amfani da shi a kamfanin lemuka a Ingila (masu yin Tonic Water) da Amurka (masu yin lemon Schweppes). Amma su wadannan kamfanonin ba wai suna sa wannan magani domin ya kiyaye mu daga maleriya ba ne, a’a sai saboda dadin dandanonsa. Domin abin da suke zubawa a kowace kwalba bai wuce maki 80 a ma’aunin na milligram ba. Amma a ka’ida idan mutum zai sha maganin chlorokuine domin kiyaye kamuwa daga ciwon maleriya sai wannan maki ya nunka kusan sau biyar zuwa goma.

To wannan ne ya kan sa wasu suke samun kaikayin jiki idan sun sha lemon Schweppes, wato wannan sinadari da akan dan sa kadan shi ke sa musu kaikayin. Da fatan kin fahimta.

Mene ne maganin tsutsar ciki ne? Domin na gwada wasu a nan amma ba canji.

Daga Lawal, Lagos

Amsa: Ba canji kamar yaya? Ba fa dole ba ne sai ka ga tsutar cikin a bayan gida ba, domin za su iya fita ba ka sani ba. Ba a kuma tabbatar mutum na da ciwon sai ya gan su kuru-kuru a bayan gida, ko idan an auna bayan gida an ga kwayayensu. Don haka idan ba tabbatarwa aka yi kana da su ba, alamun da kake ji zai iya zama na wani abu daban, ba tsutsr ciki ba.

Amma dai da yake magungunan za ka iya samunsu ko da a kyamis ne, yana da kyau ka san akwai nau’i daban-daban, wadanda aka fi samu su ne mebendazole da albendazole, wadanda idan ka saye su za a maka bayanin yadda ake amfani da su. Muhimmi dai daga ciki shi ne ka samu ka kara sha bayan sati biyu kafin a ce ka sha maganin yadda ya kamata.

Ina da kurajen fuska ina masu magani suna mutuwa amma tabon ba ya tafiya. Duk wurin ya yi baki da tabo. Shi ne na ke neman shawara

Daga A.M

Amsa: E, ai in dai ba daina fitowa suka yi ba da wuya ka rabu da tabo saboda shi tabon ya fi kurjin samun wurin zama, domin sai ya dau shekaru bai bace ba. Don haka sai an shawo kan kurajen gaba-daya kafin ka nemi tabon ka rasa. Zan iya cewa shawara ita ce ka nemi likitan fata kwararre wanda zai rubuta maka har da na rage tabo.

Mai ciwon kunne da ruwa ke fitowa idan ba a je asibiti ba aka rika cin abinci lafiyayye za a dace?

Daga Aminu, Sokoto

Amsa: A’a, a likitance mai ciwon kunnen da yake ruwa ba a masa magani ba zai iya kurmancewa. Wato ciwon zai tsaya amma sai ya tabbatar ya cinye ko lalata kayan ji na kunnen. Wannan idan ma diwar ba ta shiga kwakwalwa ba kenan. Daga ciwo a samu nakasa kenan.

Idan na ci abinci na kan samu hararwa? Shin hakan matsala ce?

Daga Muhammad S.

Amsa: E, matsala ce, bai kamata a samu hararwa idan aka gama cin abinci ba, sai dai fa idan cin keta aka yi wa abincin, to ciki fa dole ya dawo da abinda ba zai iya dauka ba. Idan kana yawan samun haka matsala ce da ke bukatar ganin likita.

Wane irin abinci mai ciwon suga zai ci?

Daga M. I

Amsa: Ka san abinci aji-aji ne: akwai mai kara kuzari (kamar shinkafa, garin rogo, da doya da sukari), akwai mai maiko (kamar man gyada da kakide), akwai mai bitaman (kamar ganyaye da kayan itatuwa), akwai mai gina jiki (kamar nama, kifi, wake). Mai ciwon suga zai iya cin duk wadannan abinci in banda na ajin farko mai kara kuzari, wanda ake so a rika ci dan kadan a rana, musamman ma shi kansa suga da kayan shaye-shaye masu suga, duk kamata ya yi ya ajiye.

Ko naman rago yana da wani amfani a jikin dan Adam? Kuma ko shin yana da illa?

Daga Maryam Maraba

Amsa: Naman rago yana da amfani a jiki, domin yana cikin ajin abinci mai gina jiki, wato zai iya kara gina naman jiki da saurin girma ga yara da wadanda suke da rashin kumari, ga kuma sinadarin iron mai kara jini. Sai dai kamar sauran abinci, idan nama ya yi yawa yakan yi illa domin kitsensa yana zama a jiki ya zama teba. Don haka sai an saisaita yawansa. Ga yara da marasa kumari za su iya ci su koshi, amma a manya da masu jiki, yanka biyu zuwa uku a rana ya wadatar, su ma amma ba wai dole sai an ci kullum ba.