✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wai da gaske akwai Ma’askin Dare?

Ni dai na kasance gashin kaina cikakke ne, amma daga na canza wurin aski sai na ga sumata wani bangare ya fito, wani bangare bai…

Ni dai na kasance gashin kaina cikakke ne, amma daga na canza wurin aski sai na ga sumata wani bangare ya fito, wani bangare bai fito ba. Shi ne abokai na ke cewa wai ma’askin dare ne. Ko a kimiyance haka ne?

 

Amsa: A kimiyyance babu ma’askin dare, amma akwai matsalar da kan kawo wannan abu da mutanenmu ke kira ma’askin dare. A kimiyyance sunan matsalar alopecia areata, wato cinyewar suma a wasu bangarori na kai, wanda yake kama da sanko amma ba sankon ba ne, tunda shi yana tsallake gashi, ba kamar sanko da kan ci wuri mai nisan zango tashi guda ba. Abubuwa da dama kan kawo wannan matsala, tun daga mutuwar kwayoyin dake tsuro da gashi har zuwa shigar kwayoyin cuta cikin fatar kai, zuwa shan wasu nau’ukan magunguna. Kuma zai iya shafar har ma mata, ba maza kadai ba.

To da yake naka kusan ka ce sai da ka canza wurin aski sa’annan ya fara maka to watakila kwayoyin cuta ne; idan har kwayar cuta ce kenan kusan a iya cewa za a iya hasashen makero, wanda kwayoyin cutar fungus ke kawowa. Ka san su ma kwayoyin cutar dake sa makero haka suke cin gashi taro-taro suna tsallake wani wuri suna cin wani. Don haka idan dai hakan ne ka ga suna bukatar magani kenan kafin su rabu da kai, tunda ka san makero idan ba a masa magani na gaske ba, ba ya tafiya.

Ko ma dai makeron ne, ko ma wani abu daban, shawarar da zan baka ita ce cewa ka daure ka ziyarci asibitin koyarwa na nan Sakkwato bangaren likitocin fata, su duba sumar da fatar su gani ko akwai alamun kwayoyin cuta, ko kuma sankon ne ya fara kama ka.

 

Me yake sa cin ruwa a kafa? Kuma mene ne maganinsa?

Muhammadu Ginsawa, Tofa

 

Amsa: Su ma cin ruwa matsala ce da kwayoyin cutar fungus ‘yan uwan wadancan masu kawo makero kan kawo. Ita ma sai an yi da gaske take tafiya saboda kwayoyin cutar suna da saurin jure wa magani. Da fari idan an samu irin wannan, ba laifi a ziyarci kyamis a karbi maganin shafa na cin ruwa a gwada yadda aka rubuta a jikin takardar. Idan sun tafi shikenan, idan ba su tafi ba kuma dole sai an hada da ganin likitan fata wanda zai duba ya ga ko sai an hada da kwayoyin sha.

 

Ni kuma ko za a gaya mini mene ne ke kara cikin makogarona kwi-kwi idan ina barci? Matsalar har ta kai ina damun abokai na.

Daga Mubarak A.

 

Amsa: Munshari ne ba wani abu ba. Ka san munsharin kala-kala ne. amma dai idan abokan sun damu sosai sai su hada maka kudi ka je ka ga likitan makoshi na ENT wanda zai leka makoshin ya ga ko akwai abinda za a iya yi. A kwanakin baya can mun taba bayanin munshari muka ce akwai magungunansa iri-iri tun daga takunkumin daurawa a haba, zuwa kwayoyi zuwa ‘yar karamar tiyata a makoshi, wanda sai likitan makoshin ne zai fada maka wanne ne ya dace da kai.

 

Shin me ke sa wa ne a wasu lokuta cikina ya rika ciwo yana kullewa kamar zan mutu?

Daga Abba A.A

 

Amsa: Amma dai Mallam Abba ka ba ni mamaki, abu na maka ciwo kamar za ka mutu ka rasa inda za ka zo sai shafin jarida? Lallai kana daukar lafiyarka da wasa. Ai ciwo da mutum zai ji kamar zai mutu ba sai an gaya masa inda zai nufa ba. Da ma cewa ka yi an maka maganin matsalar ne kuma ta yi sauki, kana son karin bayani abubuwan da ke kawo kullewar ciki irin wannan, to ai ka ga da mun yi hirar sosai.

 

Ko me ke kawo ciwon kugu?

Daga Auwalu, Barkum

 

Amsa: Abubuwa da dama ne kan iya kawo ciwon kugu, tun daga buguwa, zuwa ciwon koda, ko shigar kwayoyin cuta kodar da mafitsara, zuwa yawan zama na tsawon lokaci, da rashin motsa jiki da ma uwa-uba kiba.

 

Ko me ke sa mutum ya ji ana masa yawo a ciki kamar yawon tana?

Daga Abdullahi A. Mashi

Amsa: In dai ba ka shan magungunan tsabtace ciki daga cutukan macizai da tsutsotsin ciki ba abin mamaki ba ne ka rika jin haka. Wasu idan ana maganar macizan ciki sai su dauki abin kamar almara. Ka nemi maganin macijin ciki a kyamis ka sha na kwana uku, bayan sati biyu ka koma ka sake haka ka ji ko zai daina. Idan bai daina ba kai ma ka san akwai sauran aiki kenan banda wannan shan magani. Idan kuma ya daina haka za ka ci gaba da yi a kalla sau daya a shekara.

 

Mene ne kan kawo wa wasu ke samun faso da kaushi? Kuma ya za a kare matsalar?

Daga Nasir Kainuwa, Hadejia

 

Amsa: Ita ma wannan tambaya an taba amsa ta a baya. Amma dai abinda ke kawo kaushi a takaice shi ne bushewar fata da bushewar yanayi. A yanzu da yanayi ya canza ba ruwa, iska ba danshi to a yanzu ne masu busasshiyar fata ke samun kaushi da faso, yawanci kuma masu fata mai maiko ba su cika samu ba. Sai kuma nauyin jiki, domi masu nauyi ma idan suna da busasshiyar fatar kafa, kafar za ta iya tsagewa saboda nauyi.

Hanyar da za a kare kai kuwa ita ce mutum ya san irin fatarsa, idan busasshiya ce ya rika lullube ta da mai, mai danko kamar basilin, ya kuma rika nadeta cikin safa a ko da yaushe