Jam’iyyar APC a Jihar Legas ta sanar da dakatar da harkokin yakin neman zabenta saboda wahalar man fetur da ta kudin da ake fama da ita a Najeriya.
Shugaban jam’iyyar a Jihar, Cornelius Ojelabi, ne ya sanar da hakan ranar Talata, inda ya ce daukar matakin ya zama dole la’akari da halin da ake ciki a halin yanzu.
- Turkiyya ta ayyana dokar ta-baci ta wata 3 a yankunan da girgizar kasa ta yi barna
- NAJERIYA A YAU: Yadda harkar Kudi ta intanet ta Sa ’yan Najeriya tafka asara
Sanarwar ta kuma jajantawa talakawa wadanda suka fada cikin mawuyacin hali sakamakon yanayin da suka tsinci kansu.
APC ta ce zai zama alamar rashin tausayi idan ta ci gaba da harkokin yakin neman zaben a Jihar ba tare da la’akari da halin da ’yan kasa ke ciki ba.
Cornelius ya kuma ce hatta mabobin jam’iyyar ta APC ba su tsira daga wahalar rashin kudi da ta ta fetur din da sauran ’yan kasa ke sha ba.
Daga nan sai ya bi sauran ’yan kasa wajen kira da a tausaya wa jama’a wajen sake duba manufar canjin kudin.
Ya kuma roki dillalan man fetur din da su saki man yadda ya kamata saboda kaucewa yi wa zabe mai zuwa zagon kasa.