Sahun farko na ’yan Najeriya da aka kwashe daga Sudan bayan barkewar yaki sun sauka a Abuja a cikin daren Laraba.
A halin yanzu wasu jiragen sun nufi kasar Masar domin jigilar ragowar ’yan Najeriya — dalibai da mazauna kasar Sudan — daga kasar Masar da suka tsallaka bayan kwanaki cikin tsaka-mai-wuya.
- Lokaci ya yi da Musulmai za su samar da ‘Mulliywood’ – Furodusar ‘The Two Aishas’
- EFCC ta karbe gidaje 324 a Kano
Sai da suka shafe akalla kwana hudu a kan iyakar kasar Masar kafin su samu izinin shiga, bayan da hukumomin leken asirin Najeriya suka sa baki.
Yakin da ya barke a Sudan ranar 14 ga wata Afrilu ya ci gaba da kazancewa, lamarin da ya sa gwamnatin Najeriya ta bukaci ’yan kasarta da ke can su hadu a birnin Khartoum domin a kwaso su gida.
Hana tashin jirage bayan kazancewar yakin ta sa Ma’aikatar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya suka tsara cewa kwashe ’yan kasar daga Khartoum a cikin motoci zuwa kasar Masar, inda daga nan jirage za su kwaso su zuwa gida.
Sai dai tun kafin a lokacin da aka je kwashe sahun farko na ’yan kasar aka yi ta samun takaddama, inda motoci suka ki daukar jama’a cewa ba a cika musu su kudin aikinsu ba.
Bayan tafiyar kusan awa 12, a hanyar iyakar Masar da ke Aswan direbobi suka yi wastsi da su cewa ba a cika musu kudin aiki ba.
Hukumar ’Yan Najeriya da ke Kasashen Waje ta ce Hukumar Agajin Gaggawa ta shawo kan lamarin an ci gaba da tafiya.
Sai dai kuma an sake samun irin wannan dambarwa, kafin a samu da kyar suka ci gaba da tafiya ta kusan awa 18.
Tsugune ba ta kare ba, daga karshe hukumomin kasar Masar suka hana su shiga kasar bisa hujjar rashin takardu da cika ka’idojoji.
Wanna abu na faruwa ne a yayin da ake gab da karewar wa’adin tsagaita wuta da bangarorin da ke yaki da juna a Khartoum suka sanya.
Wadanda suka rage a Khartoum kuma sun kara shiga tsaka mai wuya inda suka zargi jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya da ke can da tserewa da iyalansu su bar su.
Amma daga bisani ofishin ya bayyana cewa jami’ansa na nan, ba za su bar kasar ba sai an gama kwamshe daukacin ’yan Najeriya.
Gwamnati ta kuma bayyana cewa tana kokarin ganin an sasanta domin hukumomin Masar su bar wadanda ke iyakar kasar su shiga domin hawa jirgi zuwa gida.
A can Khartoum kuma, bayan rukuni na biyu motoci sun zo, sai bayan da aka yi lodi, mutane sun gama hawa mota, direbobi suka ce babu inda motocinsu za su motsa sai an ba su kudi.
Shi ma haka aka yi ta ce-ce-ku-ce, kafin daga baya ofishin jakadancin da ke can ya fito ya bayyana cewa ba su da hannu wajen biyan kudin motocin, aikin Ma’aikatar Kula da Agaji da Jin Kai ce take yi daga Najeriya — Su dai kawai an ba su umarnin samun motoci da tara mutane ne.
Daga baya dai an daidaita motocin sun kai su Port Sudan, inda kafin su iya aka yi watsi da su kaman wadanda suka tafi Masar.
Bayan an daidaita sun tafi kuma kafar wata mota daga cikin ayarin motoci 27 din ta kama da wuta, inda tayarta ta yi bindiga a kusa da shingen binciken ‘yan tawaye.
Sai dai mayakan sun taimaka har aka gyara motar suka ci gaba da tafiya kuma yanzu sun isa can inda aka yi musu masauki kafin shirya yadda za su dawo gida.
A ranar Talata aka kwashi wadanda ke iyakar Masar zuwa Aswan, inda jirage ke jiransu a filin jirgi.
Amma wasu suka ga samu, suka ga rashi, inda aka dawo da su sansani saboda rashi wuri a jirgi.
A ranar Laraba rukunin farko suka baro kasar Masar inda suka isa Abuja da misalin karfe 11.30 na dare.