Daya daga cikin daliban da ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC ya harbu da cutar COVId-19 a Jihar Akwa Ibom COVID-19.
An gano Dalibin da aka ce yana da kwayar cutar ya yi fice a cikin dalibai 100 dake rubuta jarabwawar da aka yi wa gwajin cutar.
Gwamna Udom Emmanuel wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da mutanen jihar ya ce dalibin ya dauki matakin da ya dace don guje wa yaduwar cutar.
Da haka ne gwamnatin jihar ta fara yin gwajin cutar a wasu makarantun sakandare, kuma ta raba takunkumi sama da 100,000 ga dukkan makarantun, tare kuma da sanya matakai don tabbatar da cewa daliban ba su rasa komai ba.
Ya ce gwamnati tana kai wa makarantu ziyara don tabbatar da cewa daliban da ke rubuta WAEC lafiyan su klau ..Gwamnati sun gwada dalibai sama da 100 kuma mutum daya ne aka samu da cutar ta covid
“Mun yi abin da ya kamata mu yi ta hanyar lafiya, ina so in yi imani da cewa yanzu, saurayin ya samu lafiya.
“Dukkan su suna cikin koshin lafiya.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci makarantar sakandaren Al’umma, Garuruwa hudu a Uyo, da sauransu, Mataimakin Shugaban makarantar, Misis Idorenyin Otuekong, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta ba da kyakykyawar fuska ga dukkan daliban da ke rubuta WAEC.Ta kara da cewa daliban suna bin ka’idojin COVID-19 a makarantar kuma gwamna ya Tanada musu abubuwan don kare kansu