✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadansu Fulani sun halaka dan uwansu suka turbude shi kasa

Dubun wasu matasan Fullani makiyaya ta cika, waɗanda ake zargi da kashe magidancin Bafulatini mai suna Usman Muhammad bayan da ya nemi taimakonsu a kan…

Dubun wasu matasan Fullani makiyaya ta cika, waɗanda ake zargi da kashe magidancin Bafulatini mai suna Usman Muhammad bayan da ya nemi taimakonsu a kan su yi masa rakiya zuwa sabon wajen da yake fatan komawa da dabobbinsa domin kiwo.

Majiyarmu ta shaida mana cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan da ya gabata,  bayan da matasan Fulanin masu suna Abubakar Abdullahi da Tayo Muhammadu suka yi yarjejeniya a tsakaninsu da marigayin, inda bayan da suka yi nisa a tafiyarsu ne sai suka yaudare shi, suka halaka shi, suka haƙa rami suka jefa shi a ciki. 

Majiyar ta ce matasan Fulanin sun binne mutumin da suka kashe ne suka bar hannunsa a waje. An gano gawarsa ne bayan kwana biyar da faruwar lamarin. Kamar yadda ɗaya daga cikin matasan ya shaida, ya ce a lokacin da suke ƙoƙarin halaka shi, ya tabbatar masu cewa dukiyarsa ba za ta ciwu a wurinsu ba, don haka su kai wa ɗan uwansa domin yana da iyali da ’ya’ya magada.

Asirin matasan ya cika ne a daidai lokacin da suke tsaka da cinikin shanu da tumakin mutumin, inda waɗanda suka kira su saya suka nemi a nuna musu mai dabobbin.

Sai dai ɗaya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Abubakar Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa saɓani ne ya shiga sakaninsa da mamacin har ta kai ga sun yi hatsaniya a taskaninsu, abin da ya kai ga kisan mamacin. Ya ce su biyun da ake zargi da kisan ’yan uwan juna ne kuma mamacin ya same su ne, ya yi yarjejeniya da su cewa za su raka shi Obada Oko, wani ɗan gari da ke wajen birnin Abekuta, inda yake so ya kai dabbobinsa kiwo domin akwai ruwa a yankin.

“Tun farko mutumin daga Ilaro ya zo, daman can akwai wanda ya yi jinga da shi ya rako daga can Ilaro zuwa Ayetoro duk a nan Jihar Ogun, bayan ya zo Ayetoro ne ya nemi mu raka shi Obada Oko, ya ce ya kira wanda ya rako shi da farko a waya ba ya ɗaga wayar, sai muka ce masa Naira dubu 20 zai ba mu ladan aiki. Ya ce zai ba mu dubu 16, nan muka amince muka raka shi. Da muka isa wurin da zai yi kiwon sai mahaifin Tayo ɗan uwan nawa ya ce ba za a haɗa shanunsa da na mutumin ba, domin shi nasa suna da ciwo kada shanun baƙon su harbu. Sai muka ƙara zuwa gaba muka sami wasu Fulani da shanunsu lafiyayyu ne. A nan ne muka ce zai zauna ya yi kiwonsa, a lokacin ya yi yunƙurin sayar da shanun, har na kira wasu mutane suka yi ciniki, “ inji shi.

Ya ƙara da cewa daga nan ne ya bar Tayo a wajan shanun sai ya ɗauki marigayin a kan babur suka tafi ya nuna masa rafin da shanun sa za su riƙa shan ruwa. “To, a hanyarmu ta dawowa ne muka faɗi a kan babur sai ya fusata, ya ce yaya nake ganganci haka? Sai ya ɗauko sanda ya buga mani, ni kuma dama ina sagale da adda a kafaɗata. Nan take na ɗauko ta na daɓa nasa, ashe a wuya na same shi. Nan da nan jikina ya yi sanyi, ya hau karkarwa. Sai  na je na samu ɗan uwana da ke wajen shanun, na shaida masa. Ya ba ni shawarar mu haƙa rami mu saka shi, mu rufe mu tafi abinmu. A lokacin da na kai masa sara ya ce ka kashe ni, ka kai wa ɗan uwana dukiyata, ina da iyali da yara magadana. ’Yan uwansa sun neme shi suka rasa, sai aka kama ni, na shaida masu cewa mun sami saɓani, mun yi rikici ya mutu.”

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun Ahamad Iliyasu  ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ba rikincin Fulani makiyaya da manoma ba ne irin wanda aka saba gani. Ya sha alwashin hukunta duk wani da aka samu da hannu cikin al’amarin.