✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wace irin kuna ke warkewa ba tare da tabo ba?

Wai shin idan mutum ya kone yana iya dawowa yadda yake kafin kunar kuwa? Amsa: Ya danganta da irin kunar da abin da ya kona…

Wai shin idan mutum ya kone yana iya dawowa yadda yake kafin kunar kuwa?

Amsa: Ya danganta da irin kunar da abin da ya kona mutum da kuma wurin da aka kone din a jiki. Domin ka san kunar mataki-mataki ce, kuma akwai matakai har uku; mataki na farko da na biyu da na uku. A mataki na farko kunar iya fatar sama ta ke ci, a mataki na biyu kuna na cin fatar sama da wani bangare na fatar tsakiya. A mataki na karshe kuma kuna na cin fatar sama da ta tsakiya da ta can kasa, har ma wani bangare na abin da ke kasa da fata kamar naman jiki.

A mataki na farko ne kawai fata kan iya dawowa yadda take bayan kunar ta warke, amma ba a iya samun waraka a dawo yadda ake a sauran matakan kunar. Misalin kuna matakin farko shi ne konewa da mukan yi a dasashi idan muka sha abu mai zafi kamar shayi, kunu, koko da romon farfesu. A wannan kuna za a dan ji saman dasashi ya tashi yana dayewa, amma bayan kwanaki biyu wurin kan koma kamar ba a yi ba. Mataki na biyu kan bar tabo wanda da kyar ne ya bace gaba daya, mataki na uku kuma yana barin katon tabo da ma tawaya ta tattarewar fata da tsoka a kasa ma amfani da sashen da abin ya faru. Sai dai a yanzu likitocin tiyatar gyaran fata na iya yin tiyata su lullube wurin da wata fata mai lafiya ta yadda tabon ba zai yi muni ba.

Wace irin cuta ce cutar Herpes?

Daga Muhammad Sani, Gabon

Amsa: Ciwon herpes wanda wasu kamusun Hausa ke kira ciwon bulaliya, ciwo ne da kan sa fesowar kuraje a gadon baya da kirji da fuska a wasu lokuta a manya, wanda ke kama da shatin bulaliya, wato shatin kurajen na da zubi mai kamar an zane mutum da bulaliya. Shi ma za a gan shi kamar kuna amma ba kuna ba ce. 

kwayar cutar birus ce ke kawo shi, don haka ba wani magani ake masa ba har sai ya lafa. Da kansa zai tafi. Sai dai kawai a ce mutum ya je ya ga likita wanda zai tabbatar ciwon ne, ba wani abu daban ba. Idan ta kama a ba shi maganin kashe zogi, na sha, ko na shafawa, domin abinda ciwon ya fi zuwa da shi kenan; zogi a wurin da kurajen suka feso. 

Wannan kwayar cuta ita ce dai mai sa kurajen farankama wato chickenpod a kananan yara. Su kuma kurajen a yara ba sa shatin kamar bulala sai dai su yi kamar na kyanda. Duk wanda ya samu allurar riga-kafin cutar (baricella baccine) tun a kuruciya, wadda akan ba kowane yaro a jerin jadawalin allurar riga kafi, ba zai yi farankama ba ballantana ciwon bulaliyar.

Ko da gaske ne cin gauta yana sa basir?

Daga Usman Baba

Amsa: A’a ba da gaske ba ne. Ai in ban yi kuskure ba gauta busasshen data ne. Kuma mun sha saka data a cikin ‘ya’yan itatuwa masu amfani. Bambancin busasshen ‘ya’yan itatuwa a ruwan ciki ne da yawan bitamin. A busasshe ruwan da bitamin kadan ne, a nunanne kuma da ruwa da bitaman duka cikakku ne ba su ragu ba.

Wai da gaske gwanda ba ta da wani amfani a jikin dan Adam?

Daga K. Bello, Kiyawa

Amsa: A’a haba ai kai na dauka mai bin wannan shafi ne sosai. Kai idan aka ce maka gwanda ba ta da amfani za ka yarda? Haba ai gwanda na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwa ma su amfani sosai tunda tana da bitamin na rukunin C da sinadarin lycopene, sinadarin nan mai silbi da ke taimakawa wajen saurin tsotse abinci.  

Ko ana iya kamuwa da ciwon asma ta iska ne?

Daga Muhammad Auwal, Zaria

Amsa: A’a akwai kwayoyin gado da kan sa ko mutum zai samu ciwon asma, ba kwayoyin iska ba. Sai dai kwayoyin iskan kamar kura da hazo za su iya sa ciwon ya tashi ga wanda yake da matsalar 

Ko canjin iska na iya sa matsalar hauka ta kwakwalwa?

Daga S. Umar Malumfashi

Amsa: A’a shi ma yanayi ba ya kawo ciwon hauka sai dai ko gado da shan miyagun kwayoyi. Amma canjin yanayi shi ma zai iya ta’azzara ciwon. Misali masu bincike sun ce kamar yanayin sanyi yakan iya tunzura ciwon ga wanda ba ya shan magani.

Shin da gaske ana so mutum ya rika shan maganin wanke ciki. Wasu sukan sha sai a ga suna gudawa, wai sun wanke cikinsu.

Daga A.A Tela

Amsa: A’a ba a so mutum ya nemi wani abu na magani mai wanke ciki da ya wuce wadanda aka halitta mana na ‘ya’yan itatuwa da ganyaye, wadanda su ne abinci masu wanke ciki banda kuma kara mana sinadaran bitamin da suke yi. Duk wanda ya je ya sha wani maganin wanke ciki ya je ya masa illa (kamar irin wannan gudawa da ka ce suna sa wa), shi ya jiwo. 

Ina so a yi wa mata da maza kashedi akan illar shafe-shafe da irin mayukan da ya kamata a rika shafawa

Daga Abdul Abdul, Gwangwan da Muhammad K.M

Amsa: E, da kuna binmu ai da kun san cewa an sha magana akan wannan. Yawanci illar a sinadaran da akan hada wadannan mayuka da su ne, irinsu hydrokuinone  da mercury da cysteamine masu bata koda. A wasu lokuta akan boye sunayen wadannan sinadarai, saboda haka idan baka sansu ba da wuya ka gane, don haka kawai mutum ya nemi man shafawa irin wanda aka sani cewa ba sa bata fata irin masu dankon nan ko wadanda aka rubuta suna da bitaman mai gyara fata kamar bitamin E, ko man kwakwa da sauran dai wadanda aka san da wuya su bata fata. Wannan shi ya fi.