✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wace irin batar basira ce haka?

Tun bayan kafuwar Gwamnatin Nasir el-Rufa’i a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 hankulan malaman makarantun firamare a Jihar Kaduna ba su kwanta ba,…

Tun bayan kafuwar Gwamnatin Nasir el-Rufa’i a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 hankulan malaman makarantun firamare a Jihar Kaduna ba su kwanta ba, a kullum sai sun yi ta gamuwa da matsalolin da ke addabarsu, suna kara tsoma su cikin koramar wahalar da aka rigaya aka jefa su a ciki. 

Da farko dai an bullo da wani tsarin da ya muzguna musu ainun na tantance  malaman bogi daga cikinsu, aka yi wata-da-watanni ana binciken da bai taimaka da komai ba. Daga bisani kuma aka nemi a tabbatar da  cancantarsu  ta yin aikin malanta yayin da aka bidi su nuna takardar shaidar malanta  mai darajar NCE, aka kuma rege wadanda ba su da ita, amma duk da haka nan ba a bari malaman sun sanya ransu a inuwa ba, domin kuwa hatta  albashin da za a biya su don su ji dadin ci gaba da gudanar da aikinsu cikin mawuyacin yanayi bai samuwa sam-sam. 

Wadannan ba su ne kadai matsalolin da malaman makarantun firamare suka sha fama da su ba, a ’yan kwanakin da suka gabata. An ce da yawa daga cikinsu ba su da kwarewar koyarwa duk kuwa da an tabbatar suna da takardun shaidar malanta ta NCE, wacce gwamnati ta bukata, saboda haka nan sai aka sanya su  gaba, aka ce sai an yi musu gwadawa daidai da irin jarabawar da ake yi wa ‘yan aji hudu na firamare, wanda kuma duk bai samu maki saba’in da biyar cikin dari (75/100) ba za a sallame shi. Ilai kuwa hakan aka yi. An ce malaman makarantar sun zauna jarabawar da ba a san wanda ya tsara ta ba, kuma an samu guda dubu ashirin da daya daga cikinsu da suka kasa  samun nasara, saboda haka nan an ce za a  kore su don a maye gurabansu da wasu sababbi har guda dubu ashirin da biyar.  

Wannan babbar magana ce da ta tayar da hankulan daukacin jama’ar Jihar Kaduna, domin korar malaman makaranta sama da dubu ashirin al’amari ne da zai iya jefa mutane sama da dubu dari da suka dogara a kansu cikin wata sabuwar ukubar rayuwa wacce ba ta iya misaltuwa, sa’anan kuma daukar wasu malaman can daban ba dabara ce ta magance wannan matsalar ba, domin daga karshe za a gano cewa an gudu ne  ba  a tsira ba, domin kuwa ai ba daga sama ne sababbin malaman da za a dauka za su fado ba, su ma fa ’yan Najeriya ne, suna iya  kasancewa irin wadancan  da  za a  kora domin kuwa  babu alamun cewa an magance matsalolin da suka haddasa haka. Ai yadda dillin-takan-yi-dillin-haka-ma-dillin-takan-yi-dillin. Ai inda tunkiyar gaba ta sha ruwa nan ne ma na baya za ta sha. Idan har an sake sababbin malaman za a canja yanayin da tsofaffin da aka sallama suka yi aiki ne a ciki? Za a inganta yanayin makarantun ne da kuma kyautata hanyoyi da dabarun koyarwa da kuma yi wa malaman ihsanin da ya kamata don karfafa musu gwiwa?  

Shin an tsaya an binciki yanayin da malaman ke aiki da kuma kokarin gano dalilan da suka sa malamin da ke da takardar shaidar NCE zai kasa cin jarabawar ’yan aji hudu na firamare? Ai daga ji ma an san shero ta aka yi; wayon a ci ne dai zai sa a kori kare daga gindin dunya. An ce wai sababbin malaman da za su maye guraban wadancan ba lallai sai ‘yan Jihar Kaduna za a dauka ba, wanda duk ya dace, kuma  daga ko’ina ne za a dauka. To idan kuwa haka ne ashe za a kara kashe harkar bayar da ilmi, tun daga matakan farko a Jihar Kaduna, ta hanyar barin koyarwa a hannun malaman da ba su fahimci al’adu da dabi’un al’ummar da suke  ciki ba, kuma haka zai sa kananan yaran da suke koyarwa su kasa fahimtar dabi’u da al’adun iyaye da kakanninsu  tun suna cikin kuruciyarsu.

Wai shin ma  wacce hukuma ce ta rubuta wa wadancan malaman  jarrabawar, kuma su wane ne suka dudduba, suka ba su makin da suke gani sun cancanta? A batun harkar malanta dai akwai wata hukumar gwamnati da ke kula da dukkan al’amuran da suka shafi malaman makarantun firamare da na sakandare da ake kira National Teacherts Institute, watau NTI. An waiwaye ta wajen rubuta  wa malaman jarrabawar da suka dauka da kuma fitar da sakamakonta?  Idan kuma za a dauki sababbin malaman da za su maye gurbin wadancan da aka sallama, bai kamata ba a nemi National Teacherts Institute don tsara  musu wata  jarrabawar da za ta nuna kwarewarsu a zahiri? Idan kuwa haka ne, to ina ranar takardun shaidarsu ta malanta ko kuma digirin da suke da shi daga jami’a? Ana iya cewa duk na bogi ne?

An dai ce idan gafiya na da sata, daddawa ma fa wari ke gare ta, idan har an ga laifin wadancan malaman makarantar wajen kasa cin jarabawa sai kuma a waiwayi gwamnati don a fahimci inda ita ma halayenta suka taimaka musu kasancewa haka. Sanin kowa ne dai makarantun firamare a Jihar Kaduna na cikin wani mawuyacin halin rashin gyara da kuma kayayyakin aiki, sa’annan kuma malaman haka nan aka bar su kara zube, ba a daukar wani matakin inganta matsayinsu ta hanyar tuttura su kwasa-kwasai ko tarurrukan kara wa juna ilmi, sa’annan kuma uwa-uba, sai malami ya  yi shekara da shekaru bai motsa ba daga matsayin da yake, alhali kuwa takwarorinsu na wasu ma’aukatun gwamnati na ta samun karin girma a-kai-a-kai.

Haka nan kuma sa’ilin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta batar da Naira miliyan dubu goma cikin watanni takwas don ciyar da dalibai, haka nan malaman ke kallon ’yan makaranta suna  ci har sai sun yi hani’an, amma su kuwa  sai dai su yi ta buga  hamma, domin sun baro gida ba su karya kumallo ba, kuma  ba su bar wa iyalansu komai ba domin ba a biya su albashi ba. Idan da an yi amfani da wasu daga cikin wadancan miliyan dubu goma din don inganta matsayin malamai da biya musu bukatunsu a bakin aikinsu ai da  yanzu babu wasu malaman makarantun firamare da za su fi na Jihar Kaduna kwarewa a duk fadin tarayyar kasar nan.  Ashe  ke nan ana iya cewa da gangan ne gwamnati ta dauki matakan da suka janyo tabarbarewar ilmi a Jihar Kaduna, sa’annan kuma take fakewa da batun rashin kwarewar malamai don ta kawar da zargi daga kanta.  To, tun da dai gwamnati ta gwammace ta kori wadancan malaman har dubu ashirin a tashi guda, domin ta san inda za ta samu makwafinsu, sai kawai a ce  wannan  wace irin batan basira ce?