A al’ada ta dan Adam yana son tufafi mai kyau, domin ya sani tufafi mai kyau yana kara wa mutum kima da martaba, hakan ne ya sa shi sanya tufafi mai kyau da zai kayatar. Tabbas akwai damar zaben tufafi mai kyau, kuma hakan ba laifi ba ne, shi ya sa ake cewa idan kana da kyawu to ka kara da wanka.
To, haka ita ma mace take, ana so ta zama mai kyau, domin ba lallai ba ne sai an auri mummuna ko wata burtuntuna, don haka lura da kyawu din ba laifi ba ne.
Amma kyawu iri biyu ne: Akwai kyawu na zahiri; akwai kuma na badini. Abin da aka fi so shi ne, ya zamana an hada duka biyun, saboda shi kyawu na zahiri yana dusashewa matukar babu kyau na badini, sai ya zama tamkar na wucin gadi ne, domin cikin kankanen lokaci zai koma tamkar na dan maciji, ka ga dan maciji ai yana da kyau, zai rika sheki gwanin ban sha’awa.
Don haka idan ba kid a kyawu to ki tabbata kin mallaki kyawun badini, hakan zai taka rawa wurin dauwamar da kimarki a zuciyar abokin zamanki. Kada ki kasance don kina da kyawu, amma kuma ki rika sarin mijinki. Wadansu mazan sun fi son fara kyakkyawa; wadansu kuma sun fi son baka kyakkyawa. Hausawa suna cewa: Ido wa ka raina? Sai aka ce wanda nake gani kullum, domin duk kyawun ki daga kin yi aure, yau da gobe mijinki zai daina ganin kyawunki, abin da zai rage har kuma ya rika ba ki daraja a wurin mijinki shi ne: Kyawun hali, domin idan kyawu na zahiri ya hadu da kyawun hali, da kuma kyautatawa to wannan ne zai ba mutum kariya wajen ganin wancan kyawu kullum yana nan. A lokacin da kika rika kyautata wa mijinki, kyawunki ba zai gushe ba, amma a lokacin da kika munana wa mijinki, to komai kyawunki na zahiri sai ya gushe a idanu da kuma zuciyar mijinki. Saboda duk lokacin da mace ta munana wa mijinta, to bakikkirin zai rika ganin ta, zai ga babu wani annuri a tare da ita.
Mace kamila ita ce wacce idan mutum ya kalle ta zai samu natsuwa, kamar yadda Amirul Mumina Ali yake cewa: “Na kasance da na kalli Fatima Azzahra, sai inji damuwa da bakin ciki sun tafi.” Saboda ita Fatima ta hada duka biyu; kyawu na zahiri da na badini. Ga bangaren maza kuma lallai akwai muhimmanci mutum ya tsaya ya zabi wacce ransa ya kwanta da ita, ba wai ka auri wacce da ka kalle ta ka ji ba ka son karawa ba, a’a yi kokari ka samu wacce da ka kalle ta za ka kara samun natsuwa da kwanciyar hankali.
Don haka lura da kyawun mace yana daga cikin abubuwan da ma’aki (SAW) ya yi kira gare shi, inda yake cewa “Idan dayanku yana so ya yi aure to ya tambayi gashinta, kamar yadda zai tambayi fuskarta domin gashi daya ne daga cikin abubuwa masu kyawu guda biyu wato (kyan fuska da gashi)”.
Wannan Hadisi yana yi mana bayani ne a kan cewa kamar yadda mai neman aure yakan nemi mai gashi, to neman kyawu shi ma babu laifi. Babban abin da ake bukata shi ne ka auri matar da za ta debe maka kewa, ba wai a ce ka yi aure ba, amma bai hana ka zaman dandali ba, sai ka ga wasu sun zauna zaman majalisa babu abin da suke illa kallon mata, wanda hakan haramun ne.
Babu shakka zabin kyakkyawar mace yana daga cikin dama da yanci da mai neman aure yake da shi, domin da zabin kashin kai ne ake samun nagartacen aure mai karko da dorewa, ba wanda ake tilasta maka ka aura ba. Allah Ya agaza mana.
080 60651676
Email – [email protected]
Wace ce mace mai kyau?
A al’ada ta dan Adam yana son tufafi mai kyau, domin ya sani tufafi mai kyau yana kara wa mutum kima da martaba, hakan ne…