Jama’a da dama sai yawo da maganganu suke yi cewa, ba su gane inda gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanya gaba ba a karkashin jagorancin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, wanda ake kallon na da cikakiyar kwarare da gogewa da basirar mulki da zamantakewar al’umma.
Su kuma masu kare gwamnatinsa cewa suke ya kamata mutane su jira su ga lokacin nada sababbin kwamishinoni, inda ta nan za a iya gane inda alkiblar gwamnatin ta sanya gaba. Sun ce idan gwamnatin ta nada mukarraban da za su taya ta aiki ne za a gane ko za ta iya dorawa a kan ayyukkan da gwamnatin Bafarawa da ta Wammako suka yi a jihar na ciyar da al’ummarta gaba ko a’a.
To, sai dai yanzu sama da watanni da nada kwamishinonin inda ake tsammanin abubuwa za su kankama, amma shiru babu wani sauyi, tamkar an aiki bawa garinsu.
Masu cewa ba su gane alkiblar Gwamna Tambuwal ba, suna cewa, shi kansa Gwamnan tunda aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, kawo yanzu bai taba zama na mako daya a cikin jihar ba, inda wasu suke cewa sau daya ya taba yin kwana hudu jeri a jihar. Akwai masu zargin cewa ya fita zuwa kasashen waje sau 80 daga rantsar da shi zuwa yau.
Wani muhimmin abin da ya fi daukar hankali da tunanin jama’ar jihar shi ne, yadda aka gudanar da zabubbukan fitar-da-gwani na masu neman tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomi 23 na jihar.
Zabubbukan da ake zargin Gwamnan ya bai wa wasu manyan jihar damar yin yadda suke so, koda kuwa lamarin zai iya samar da baraka, ko rarrabuwar kawuna a tsakanin ’ya’yan Jam’iyyar APC mai mulkin jihar. Wadannan zabubbuka tuni jama’a suka ce, ba a yi su yadda ya kamata ba, kuma sun saba wa dimokuradiyya.
Gwamna Tambuwal dai ya yi alkawari ga jama’ar jihar cewa, al’umma ne za ta zabi wadanda suke so, shi babu wani dan takara da yake goya wa baya. To, amma tun daga tashin farko jama’a suka soma zargin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don sasanta ’yan takara domin kauce wa samun baraka, inda aka zargi kwamitin da mara wa wadansu ’yan takara baya.
daya daga cikin misalan inda ake zargin haka ta faru shi ne yadda aka gudanar da zaben fitar-da-gwani a karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, karamar hukumar da ke da matsayi da kima a jihar kasancewarta fadar jihar.
Abin da ya bayar da mamaki shi ne, yadda ’yan siyasar yankin manya da matsakaita suka dunkule waje daya suka mara wa wani dan takara, wanda kuma ba shi al’ummar karamar hukumar ke so ba. Amma sai ga shi wannan dan takara, bai samu kuri’un da za su ba shi nasara ba, wanda jama’a ke so ne ya samu kuri’un da suka ninka na dan takarar manyan. Kuma hakan ne ya sa ake zargin wani dan Majalisar Dokokin Jihar ya harzuka ya karbe kuri’un da aka kada ya yayyaga su a gaban jama’a.
Abubuwa dai da dama sun faru, wadanda ba su da dadin ji a wannan zaben musamman matsayin da wadanda ake zargi da aikata su ke da shi a tsarin dokokin kasa da jam’iyya. Kuma hakan ya harzuka magoya bayan dan takarar ya fi yawan kuri’u suka fusata, har suna fadar cewa, an yi musu PDP (zalunci) kuma Jam’iyar PDP ce ke dauke da tambarin APC, domin abubuwan da aka yi wa Abdullahi M. Hassan tamkar Jam’iyyar PDP ce ke mulki a jihar.
Wasun na cewa, babu dalilin da zai sanya dan majalisa ya yaga kuri’a domin tsoron faduwar dan takarar da yake mara wa baya, kuma a hana jami’an tsaro su kama shi, sun ce in da a ce wani mutum da ba ya rike da wani mukami ya aikata haka da tuni jami’an tsaro sun hada masa jini da majina. Abin da aka rika fadi tun a wurin shi ne wai shi yaron Sanata Wamakko ne ba abin da za a yi masa, koda ya aikata fiye da haka.
Sanata Wamakko mutum ne mai son zaman lafiya, kuma har saukarsa mulki bai biya jama’ar karamar hukumar bashin goyon bayan da suka ba shi ba, ta yawan kuri’un da suka kada masa a karo na biyu na takararsa Gwamna da lokacin zabensa a Sanata da kuma zaben dan takarar da ya tsayar a kujerar Gwamna wato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sakkwato).
Zuwan Abdullahi M. Hassan a matsayin Shugaban karamar Hukumar ne ya fitar da su kunya ta wajen yi wa jama’ar yankin ayyukkan raya kasa a kowace mazaba, amma a ce wai Sanata Wamakko yana cikin wadanda suka sanya hannu da hana wannan bawan Allah ya sake komawa kan mulki.
Jama’ar karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa suna sanya rai Gwamna Aminu Tambuwal ya yi hobbasa don kawo karshen wannan rigima ta hanyar share musu hawaye, musamman da suka ji labarin cewa gwamnatinsa ta kafa kwamitin sauraron korafe-korafen jama’a a kananan hukumomi daban-daban.
Akwai masu bayyana Gwamna Aminu Tambuwal da wanda ya kasa tafiyar da mulkin jihar kamar yadda suke tsammani. Sun ce a matsayinsa na masanin dokokin kasa, wanda ba ya son ya saba wa dokoki ko tauye hakkin jama’a, sai ga shi zaben fitar-da-gwanin neman tsayar da dan takara na neman zubar masa da kima.
Daga Lawali Bawa Ladan,
Rukunin Gidaje 500 na Sakkwato ta Kudu,
Imel: [email protected]
Wa ke mulkain Jihar Sakkwato tsakanin Tambuwal da Wamakko?
Jama’a da dama sai yawo da maganganu suke yi cewa, ba su gane inda gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanya gaba ba a karkashin jagorancin Alhaji…