Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Mosses, zai shafe watanni shida ko fiye ba tare da ya taka leda ba.
Victor Moses wanda a yanzu yake murza leda a kungiyar Spartak Moscow da ke Rasha, zai shafe watanni shidan ne ba tare da buga kwallo ba a sakamakon wani rauni da ya samu.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Najeriya Za Su Fara Yin Wayar Minti Biyu a N100
- An gurfanar da tsohon da ya yi barazanar kashe wata da adda a gaban kotu
Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi wa dan wasan tiyata sakamakon raunin da ya samu a kafa yayin wasan gasar Firimiyar Rasha da kungiyarsa ta buga ranar Asabar.
A minti na 33 ne dai Mikhail Ignatov ya canji Moses a fafatawar da Spartak Moscow ta doke kungiyar Ural da ci 2-0 a filin wasa na Ekaterinburg Arena.
Kungiyar Spartak wacce Victor Moses ke buga wa kwallo na daya daga cikin kungiyoyi da ke tashe a kasar Rasha.
Kafin kowawarsa Spartak a 2018, Moses ya taka leda a kungiyar Chelsea da ke Landan, inda ya ci mata kwallaye 18 a wasanni 128 da ta kai su ga lashe gasar Europa.
Kafin nan, Victor Moses ya ci kwallaye 12 a wasannin 27 da ya buga a yankin Afirka ta Yamma.
Ya taka rawa a nasarar da Najeriya ta samu wajen lashe kofin nahiyar Afirka (CAF) a 2013.
Tsohon dan wasan na kungiyoyin Crystal Palace, Wigan, Liverpool, West Ham, Inter Milan da kuma Fenerbahce, ya wakilci Najeria a gasar Cin Kofin Duniya karo biyu a shekarar 2014 da kuma 2018.