Allah Ya yi wa matar tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Yelwa Mohammed Danjuma Goje rasuwa a safiyar yau (Litinin) tana ‘yar shekara 55.
An samu labarin rasuwar ne daga wani sanarwa da dan tsohon gwamnan, Ahmed Mohammed Goje ya fitar, inda ya ce ta rasu ne a wani asibiti a kasar Amurka.
Hajiya Yelwa ta rasu ta bar Maigidanta, Sanata Danjuma Goje, ‘ya’ya shida, jikoki 10 da ‘yan uwa da abokanan arziki.