✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwargida: Yadda za ki tsare mutuncinki

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Abubuwan da za su taimaka wa uwargida wajen tsare mutuncinta sun hada da:
1.    Niyya: Abu na farko kuma mafi muhimmanci shi ne, daura kwakkwar niyyar bin umarnin Allah SWT game tsare mutunci. Yin niyya zai taimaki uwargida ta kasancewa cikin shirin yin abubuwan da suka dace duk lokacin da wani kalubale ya zama barazana ga tsaron mutuncinta, kuma zai taimaka mata ta iya kauce wa fitinannun abubuwa masu rage mutunci duk lokacin da suka bayyana gare ta.
2.    Kishin Kai: Uwargida za ki yi kishin kanki ta hanyar matukar jin kyamar bayyanar da wani bangare na adonki ko kwalliyarki, ko wata kawa ga namijin da bai halatta gare ki ba, ki rika jin ba kya son wani namijin da ba muharraminki ba ya ga wani bangare na jikinki, ko ya kure kusanci da jikinki ko da kuwa a bisa lalura ne. Wannan zai taimaka miki ta yadda ba za ki yi sakaci komai kankantarsa ba don ganin cewa kin tsare mutuncinki a kowane lokaci da yanayi, kuma zai sa ki zama mai yawan kaffa-kaffa da jikinki da dabi’unki da mu’amularki da maganarki don ganin cewa ba su jefa ki cikin wannan yanayi da kike kyama ba. Misalin mace mai kishin kanta ita ce wacce kwata-kwata ba ta sakin jiki da mazan da ba muharramanta ba.
 Mace mai kishin kanta ba ta bari ta saba da mazan da ba muharramanta ba har ya kasance suna raha da juna. Mace mai kishin kanta tana bakin cikin jikinta ya hadu da jikin namijin da ba muharraminta ba ko da a bisa lalura ne. In kika zama mai kishin kanki wannan zai kara miki daraja da kima a idon mutane.
3.    Takura Ma kai: Sai kin danne sha’awarki da son zuciyarki, sannan ki rika takura wa kanki yin duk abubuwan da za su tsare mutuncinki da na maigidanki da ma na iyayenki, ki kuma guji duk abubuwan da za su wofintar da mutuncinki ko na maigidanki. Ki sani, ko yaya kika yi sakaci mutuncinki zai iya zubewa, idan kika yi sakaci a hankali za ta bude duk sauran kafofin tsaron mutuncinki; kamar misalin ’yar karamar kofa a rufin kwanon daki da ke diga kada-kadan, in ba a like ta ba, a hankali za ta bata duk dakin. Don haka dole ki nesanta kanki da duk wasu dabi’u marasa kyawu da ka iya raunana miki mutuncinki da darajarki. Misalin irin haka kamar sabuwar dabi’ar da ta yadu yanzu a kasar Hausa a wannan zamani: yadda samarin unguwa ke cika gidan matan aure kuma su saki jiki har kawance ya kullu tsakaninsu, har ya kasance sun zama abokan sirrin juna. Ki sani sabo da irin wadannan samari, ko yaya karfin zumuncin da ke tsakaninku, indai su ba muharramanki ba ne, to wannan harammtaccen sabo ne, kuma yana matukar nakasa darajar macentaka, ya sa ruhinki ya zama fanko, ta yadda ita da kanta za ta daina jin kaifin macentakarta a cikin ranta,  hakan kuwa yana sa darajar aure ta sukurkuce.  
A shari’ance miji ne kadai ya halatta kalli kwalliyar matarsa, kuma haramun ne gare ta kallon kwalliyar wani namijin da ba maigidanta ba! Don haka matan aure da ke cikin irin wannan kazamar dabi’a, su yi kokari su raba kansu da ita tun kafin lokaci ya kure musu.
4.    Kiyaye abubuwan sha’awa: Uwargida ke kika san kanki, kin san abubuwan da suke zama fitina ga zuciyarki, kin san abubuwan da ka iya sawa ki ketare iyakokin Ubangiji, don haka sai kisa ido ga wadannan abubuwa kuma ki kiyaye su; ki zama mai nesanta kanki da su. In kin san zuciyarki na shagala sosai wajen kallon fina-finai, shagalar da har za ta iya haifar da wani karkataccen tunani a zuciyarki, to ya kamata ki nesanta kanki da ita, in karatun littattafan soyayya ne ke jefa zuciyarki cikin rudin alfasha, to sai ki yi kokari ki yaki zuciyarki ta hanyar daina karatun.
Haka ma za ki yaki kanki a kafofin sadarwa na zamani, ki haramta wa kanki gaisawa da maza ta cikinsu, kallon hutunansu ko yaba wani abu da suka saka ta wadannan kafafe. Ki bar sakin jiki da su kuna hira mai tsawo da haka har sabo ya shiga tsakaninku, haramtaccen sabo ne, domin kuna kara shakuwa, ana kara rubuta muku zunubi. Wannan hukunci ne da ya shafi matan Musulmi masu aure da ’yan mata.
5.    Tsare mutuncin maigida: Ki sani, mutuncinki zai samu tsaro dari-bisa dari ne kadai tare da tsaron mutuncin maigidanki, don kin tsare naki mutuncin, amma ya kasance ba ki damu da yanayin mutuncin maigidanki ba, ko ya kasance ke ce ma ke yin abubuwan da ke jaza zubewar mutuncinsa, to kamar kin rufe bangare daya na jikinki ne kin bar daya a bude. Don haka yana da mataukar muhimmanci tsare mutuncin maigida, da taimaka masa don ganin yayi kyakkyawan riko ga mutuncinsa. Za ki yi haka ne ta wadannan hanyoyin:
•    Tsare sha’awarsa: Ki kasance mai yin kokari a kodayaushe wajen ganin kin zama maganin kishir ruwar sha’awarsa, kada ya kasance saboda wani sakaci naki mijinki ya fita waje yana kalle-kallen matan mutane, ya rika tunanin da ba su dace ba a zuciyarsa; in kin yi duk abin da ya dace don ganin kin gamsar masa da sha’awarsa, to kin ba shi babbar garkuwar da za ta taimaka masa wajen tsaron ganinsa da farjinsa yayin da ya fita waje.
Wadannan abubuwa sun kunshi amsa kiransa na ibadar aure duk lokacin da ya bukata, yin kwalliya cikin irin yanayi da sigar da tafi burge shi, kula da tsabtar jiki da ta gida, bayyanar da soyayya da saukaka mu’amala da shi, da sauran kyawawan dabi’u irin na kaunatayyar auratayya.
•    boye sirrinsa gaba daya: Kada ki rika bayyanar da laifukansa, kasawarsa da kura-kurensa ga wasu mutane komai irin kusancinki da su, musamman irin abubuwan da duk wanda ya ji su sai ya ji mutuncin maigidanki ya ragu a idonsa, in ma yana da wasu dabi’u marasa kyau, to ki boye su, kuma ki zama mai yawan yin addu’a gare shi har Allah Ya sa ya canza.