✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwargida ta yi yunkurin kashe amarya

A ranar Litinin da ta gabata, a Unguwar Bakin Kasuwa, karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara; wata uwargida mai suna Yusra Alhazai ta yunkurin kashe…

A ranar Litinin da ta gabata, a Unguwar Bakin Kasuwa, karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara; wata uwargida mai suna Yusra Alhazai ta yunkurin kashe kishiyarta, amarya Shafa’atu Rilwanu ta hanyar yi mata taron dangi da abokanta, inda suka yi mata duka tare da buga mata bulon siminti a idonta, har sai da mutanen unguwar suka kwace ta. 

Aminiya ta zanta da amarya Shafa’atu, wacce ta yi mako hudu a gidan mijinta, kafin daga bisani al’amrin ya faru. “Uwargidana ba ta sona, domin tun da na shigo gidan mijina ta hade mani kai, ita da ’ya’yan mijinmu. Da ya fahimci haka sai ya ce mani, duk lokacin da ba ya gida kuma ina son hira, to in je gidan kanensa Kabiru,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa: “Haka na rika yi kuwa, sai a Litinin da ta gabata na tafi gidan; ina dawowa sai dan mijina ya ce mani munafuka. Na ce masa ni ba abokiyar yinsa ba ce. Rufe bankina ke da wuya sai kishiyata da wasu mata uku kawayenta tare da yaron suka rufe ni da duka ta ko’ina. Ta dauko bulo ta buga mani a ido, jini ya rika fita daga idon, suka yi mani tsirara. Suka yi mani wulakanci a  matancina. Ana haka mutane suka ji a waje, suka balle kofar gidan da suka rufe lokacin da suke buguna. A nan ne na samu taimakonsu, suka kwace ni, da sun kashe ni.” 

Ta ce mijin nasu ne ya kai ta asibiti, aka wanke jini aka ba ta magani suka dawo gida. Da ya kira iyayensu gaba daya domin a yi sulhu amma uwargidan ta ce ba za ta ba ta hakuri ba.

“Kwana daya da yin haka sai ’yan daba tare da yayanta Murtala Suleman, wanda ake wa lakabi da “Kwanya Wuri” suka zo unguwarmu da wukake da adduna, wai sai sun ga wanda ya tsaya mani. A haka suka sari mutum biyu, Ashiru a kai da Maniru a kafa. Da ’yan uwana suka ga haka sai suka kai maganar a wurin ’yan sanda don kwatar mani hakkina. Kwana uku muna zuwa ofishinsu, sun kasa daidaita mu, domin mai laifi ta ki yarda, don haka suka tura mu kotu.

Alkali Umar Abdullahi Zurmi shi ne alkalin kotun Shari’a ta Shinkafi. Da ya ji abin da ya faru sai ya tura kishiyar tawa gidan yari har sai na warke a ci gaba da shari’a. Bayan an tashi kotu ne aka sake ta a labarin da nake samu. 

Abdullahi Umar, mijinta bai yarda wakilin Aminiya ya tattauna da uwargidan ba, amma ya bayyana cewa: “Ba ni nan lokacin da suka yi rigimar, na samu labarin cewa fada ne suka yi da junansu har ita Shafa’atu ta samu rauni a ido. Na bukaci Yusra ta ba ta hakuri don rigimar ta mutu amma ta ki, don wai ba ita ce ta yi mata rauni ba. Na bukaci ita ma amarya kada ta je wurin hukuma amma ta ki. An je kotu alkali ya bayar da belin wadda ake zargi, cewa bayan mako biyu a dawo. Kafin a koma kotunn ina nan ina kokarin sasanta matana, domin komai ya wuce.”