Kwamitin Gudanarwa na Kasa na Jam’iyyar APC ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyar a daren ranar Litinin.
Ana kyautata zaton zaman nasu zai yanke shawara kan mutumin da jam’iyyar za ta fitar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.
- Ba mu zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takarar Shguaban kasa ba —APC
- Dole dan Kudu ya yi takarar shugaban kasa a APC —Gwamnonin Arewa ga Buhari
Ganawar tasu na zuwa ne sa’o’i kadan kafin fara zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a ranar Talata.
Mutum 23 ne dai suke zawarcin tikitin takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar.
Daga cikinsu, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru da tsohon Shugaban Majalsisar Dattawa, Sanata Kenn Nnamani sun janye.
Cuku-cukun tsayar da dan takarar shugaban kasa ta hanyar masalaha dai sai kara kamari take ta yi, tun bayan da Shugaban Kasa Buhari ya ce zai so ganin an samu haka a jam’iyyar.
Aminiya ta kawo rahoton yadda gwamnonin Arewa a karkashin jam’iyyar suka bukaci Shugaban Kasa ya zabi magajinsa, dan takarar shugaban kasa, daga yankin Kudu.
Gwamonin sun bukaci takwarorinsu da sauran ’yan Arewa su janye daga neman takarar, kiran da bisa dukkan alamu, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da Shugaban Majalisar Dattawa, ba su amsa ba.
A gefe guda kuma, bukatar da gwamnonin Arewa cewa takwarorinsu na Kudu su duba yiwuwar fitar da dan takarar daya ta hanyar masalaha na neman gagarar kundila.
Aminiya ta kawo rahoton yadda yunkurin masu fada-a-ji na APC a yankin Kudu maso Yamma na fitar da dan takara ta hanyar masalaha ya gagara.
A yayin da wadansu masu neman tikitin daga yankin ke nuna za su iya janyewa, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Uban Jam’iyyar APC na Kasa, tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwajo Bola Ahmed Tinubu sun tubure, sun nuna sai dai a fafata a akwatin zabe.
A yayin da zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ya rage kasa da awa 24 a fara gudanarwa, sai ga wani labari cewa Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar, wanda tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu yake jagoranta, ya zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Jin hakan ke da wuya gwamnoni 13 na jam’iyyar daga Arewa suka yi watsi da rahoton da ma yiwuwar zaben Ahmad Lawan dan takarar jam’iyyar.
A ganawarsu da Shugaba Buhari a ranar Litinin, gwamnonin na APC sun jaddawa mishi ce wajibi ne a bai wa yankin Kudu takarar a jam’iyyar domin kawo hadin kan kasa da adalci da kuma zaman lafiya.
Buhari dai ya shaida musu cewa shi ba shi da wani dan takara, amma yana bukatar su tabbata an fitar da dan takarar jam’iyyar ta hanyar gaskiya da kuma yin komai a fili.
Ya kuma shawarce su da su je su gana da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar kan batun da suka je mishi da shi na bai wa yankin Kudu takara.