✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta ƙone ɗanta ta soki ‘yar uwarta da wuƙa a Bayelsa

Brenda ta aikata hakan ne don yin hukunci kan laifin da yaran suka aikata mata.

Wata mahaifiyar ’ya’ya biyu, mai suna Brenda Sunday, ta ƙone ɗanta ɗan shekara bakwai da raunata ’yar uwarta mai shekara 10 da wuƙa a Jihar Bayelsa.

Brenda ta aikata hakan ne don yin hukunci kan laifin da yaran suka aikata a gidansu da ke ƙaramar hukumar Ogbia ta jihar.

Ta bayyana cewa ta aikata wannan aika-aikar ne don ɗaukar  mataki cikin fushi.

A cewarta, matakin ba da gangan ba ne, amma saboda ɗaya daga cikin ’ya’yanta ya sace kayan wani, lamarin da ta ce lamarin tsawon shekaru ya jawo mata abin kunya a matsayinta na mahaifiyarsu.

Daga bisani jami’an tsaro sun kama matar bayan da maƙwabtanta suka kai rahoton abin da ta aikata.

Kazalika, ’yan agajin sun tabbatar da ceton yaran tare da garzaya da matar zuwa ofishin ’yan sanda na Akenfa, inda aka ci gaba da yi mata tambayoyi.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda wanda a yanzu haka ake tuhumarta da cin zarafin yara.

Da aka tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar, ASP Musa Muhammed, ya ce zai bincike tare da yin ƙarin haske kan lamarin da zarar ya samu masaniya kan abin da ya faru.