✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Usain Bolt ya ki amincewa da kwantaragin Naira 54 a kulob din Central Coaster Mariners

Shahararren dan tseren duniya, dan asalin Jamaika Usain Bolt ya ki amincewa da tayin da kulob din Central Coaster Mariners na Austreliya ya yi masa…

Shahararren dan tseren duniya, dan asalin Jamaika Usain Bolt ya ki amincewa da tayin da kulob din Central Coaster Mariners na Austreliya ya yi masa na ba shi kwantaragin Dala dubu 150 kwatankwacin Naira miliyan 54.

Bolt wanda bayan ya ajiye harkar guje-guje ya rungumi  kwallon kafa, ya ce muddin kulob din yana so ya amince da tayin kwantaragin sai yak ajiye masa zunzurun Dala miliyan 3 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 830.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, Bolt wanda ya je kulob din a matsayin gwaji, a karshen makon jiya ne ya samu nasarar zura kwallaye biyu a raga da hakan ya burge mahukunta kulob din inda suka yi masa wannan tayi na Dala dubu 150 a shekara.

Yanzu dai Bolta ya ce zai karkata akalarsa zuwa neman wani kulob ne don ya ci gaba da buga kwallo.

A baya Bolt ya taba zuwa kulob din Borussia Dortmund da ke Jamus a kokaryin yi musu kwallo amma kulob din ya nuna Bolt ba irin dan kwallon da yake nema ba ne.