Hukumar Bunkasa Kasashen ta Amurka (USAID) ta tallafa wa gwamnatin Jihar Gombe da Dala miliyan 13 don samar da kwararrun malamai a jihar.
Daraktan Hukumar USAID a Najeriya Mista Stephen Haykins ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Gwamnan Jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya a Gombe.
Ya ce tuni aka fara gudanar da wannan tsari a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da Kwalejin Ilimin Kere-Kere ta Tarayya FCE (T) da ke Gombe inda Hukumar Ilimi Bai-Daya ta Jihar (SUBEB) za ta rika kula da shirin.
Mista Haykins, ya ce Hukumar USAID tana kokarin samar da wani shiri na ci gaba da zai lashe Dala miliyan100 da ake sa ran Jihar Gombe da wasu jihohin Arewa maso Gabas za su ci gajiya don bunkasa harkar noma.
Daraktan ya tabbatar wa Gwamnan cewa akwai wani shiri da a nan gaba kadan da zai taimaka wa cibiyoyin gwamnati don bunkasa harkar kula da kasafin kudi da zai sa a samu gwamnati mai inganci ta al’umma.
A cewarsa shirin yana da alaka da bangarorin samar da ruwa da inganta kiwon lafiya kuma hakan zai bai wa Jihar Gombe da sauran jihohin damar fadada al’amuransu.
A jawabinsa, Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce ganawar tasu tana daga cikin irin ayyukan da gwamnatinsa da abokan bunkasa ci gaba suke yi da za su ba su kwarin gwiwa wajen samun kudaden shiga.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa tana da manufofi da kudurce-kudurce masu kyau na ciyar da jihar gaba.