✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

United ta yi ganawar sirri da wakilin Gareth Bale

Rahotannn da ke fitowa daga Sifen sun nuna cewa Kocin Manchester United  Jose Mourinho da Darakta a kulob din Ed Woodward sun yi ganawar sirri…

Rahotannn da ke fitowa daga Sifen sun nuna cewa Kocin Manchester United  Jose Mourinho da Darakta a kulob din Ed Woodward sun yi ganawar sirri da wakilin dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen Gareth Bale.
Rahoton ya nuna wakilin Bale ya gana ne da mahukunta kulob din Manchester United a karshen makon jiya a Ingila a yunkurin ganin sun dauke Bale don ya koma United ya ci gaba da kwallo.
Bale wanda bai jin dadin yadda Ronaldo ya shiga gabansa a kulob din Madrid ba, akwai yiwuwar ya nemi canja sheka daga Madrid zuwa United a karshen kakar wasa ta bana.
Bale, mai shekara 27 bai gamsu da yadda yake kwallo a kulob din Madrid ba kuma da alama zai iya canja sheka idan ya samu damar yin haka.
Kwantaragin Bale a Madrid zai kare ne a watan Yunin 2019 wato nan da shekara uku masu zuwa.