✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

UNICEF ya naɗa Ali Nuhu gwarzon kare yara

Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya naɗa jarumin Kannywood Ali Nuhu a matsayin gwarzon kare haƙƙin yara. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms Cristian…

Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya naɗa jarumin Kannywood Ali Nuhu a matsayin gwarzon kare haƙƙin yara.

Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms Cristian Munduate ce ta bayyana haka a sanarwar da ta fitar ranar Talata a Abuja.

Ms Munduate ta ce sauran gwarazan kare yaran sun haɗa da mashiryin waƙoƙi Cobhams Asuquo, mawaƙiya WAJE, da jarumar Nollywood Kate Henshaw.

Ali Nuhu ya janye karar Hannatu Bashir

’Yan sandan Kano sun lallasa ’yan Kannywood a wasan sada zumunta

Ta ce, a tsawon shekara guda, waɗannan taurari huɗu za su yi aiki da UNICEF domin faɗakar da al’umma kan abubuwan da suka shafi yara musamman kiwon lafiya, ilimi, abinci, kariya, ruwa, da tsafta.

Wannan aiki da za su yi zai taimaka wurin tabbatar da ingantacciyar rayuwa da ci gaba mai ɗorewa ga duk yaran da aka haifa a Najeriya, in ji Ms Munduate.