Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta fitar da wani gargadi ga masu jiragen sama cewa, su sanya ido a kan fasinjoji masu shiga jirage zuwa Najeriya domin kada su dauko fasinjoji masu dauke da cutar Ebola zuwa Najeriya.
Wannan umarni dai ya fito ne sakamakon bullar cutar Ebola a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo (CDR), ta hannun Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sakamakon rahoton Hukumar Kula da Lafiyar Mutane ta Gaggawa a Kasa da Kasa (PHEIC). Sakamakon wannan gargadi da Hukumar WHO ta yi, ya sanya Hukumar NCAA ta bayar da umarni ga kamfanonin jiragen sama a Najeriya su sanya ido sosai a kan fasinjojinsu domin su tabbatar da cewa masu dauke da cutar Ebola ba su shigo Najeriya ba.
Kakakin Hukumar NCAA, Mista Sam Adurogboye, ya ce umarnin yana kunshe ne a cikin wata takarda da Daraktan Hukumar Kyaftin Mukhtar Usman, ya sanya wa hannu cewa ana umartar dukkan masu kamfanonin jiragen sama su sanar da hukumar da zarar sun dauko fasinja mai dauke da wata cuta da za a iya kamuwa da ita.
Bayanin ya ce “Dukkan kamfanonin jiragen sama su sanar da Hukumar NCAA da zarar sun fahimci sun dauko wani fasinja mai dauke da wata cuta da za a iya kamuwa da ita . Kamfanonin jiragen sama an ba su shawarar su tabbatar suna dauke da akwatin agajin gaggawa a cikin jiragensu (UPKs) kuma wanda yake dauke da maguguna na agajin gaggawa kamar yadda ke kunshe a doka.”
ShugabanHhukumar Lafiya ta Duniya Dokta Tedros Adhnom Ghebreyesus, ya ce a cikin wani umarni da ya bayar, “Lokaci ya yi da duniya za ta dauki mataki kuma mu rubanya kokarinmu a kan wannan lamari. Muna bukatar yin aiki tare domin sadaukarwa ga al’ummar kasar Kongo domin a kawo karshen wannan cuta a kuma gina harkar lafiya mai inganci. An yi aiki tukuru a bara a cikin mawuyacin hali. Ba wai Hukumar WHO ce kadai take da alhakin wannan aiki ba, har da hukumomin gwamnati da kuma al’ummomin da muke aiki kafada -da -kafada da su domin ganin an samu nasarar wannan aiki.”
Cutar Ebola a kasar Kongo ta lakume akalla rayuka 1,800 tun cikin watan Agustan bara. An kashe kudi mai yawa wajen wajen yaki da wannan cuta da kuma dakile ta amma abin ya faskara. An ayyana wannan barkewar cuta a matsayin ta biyu a duniya. Kamar yadda wani rahoto ya bayyana akwai yiyuwar kashi 90 cikin 100 na gwajin maganin cutar Ebola za a iya samun nasara. Wani gwajin sabon maganin cutar Ebola da aka yi a kan mutum biyu ya nuna sun warke daga cutar baki daya. Wadanda aka yi wa gwajin dai an sallame su daga Cibiyar Kula da Cutar Ebola da ke gabashin kasar Kongo kuma sun sake haduwa da iylansu. Rahoton ya ce kashi 90 na mutanen da suka kamu da cutar ka iya warkewa, idan aka yi musu magani a kan lokaci.
Saboda haka ya kamata Najeriya ta dauki wannan umarni na Hukumar WHO da muhimanci domin a tabbatar da wadanda suke dauke da wannan cuta mai saurin yaduwa ba su ketaro kan iyakar kasar nan ba. Ba za mu tayar da kura a kan wannan matsala ba, bayan da hukumomi cikin gida da na duniya suka fitar da gargadi. Idan za mu iya tunawa wannan cuta ta bulla a Nejeriya a shekarar 2014, ta hanyar wani dan asalin kasar Liberiya wanda ya zo halartar wani taro. Koda yake a wancan lokacin gwamnati ta dauki matakin da ya dace wajen ganin an dakile cutar, mutum bakwai ciki har da likita sun rasa rayukansu sakamakon cutar ta Ebola. A wannan lokacin ya kamata a duba yadda za a amfana da gargadin da aka yi a kan lokaci domin ganin ba a sake bari wannan cuta ta shigo Najeriya ba.
Bayan gargadi da hukuma ta yi ga masu jiragen sama, ya kamata Hukumar NCAA ta dauki wani mataki ta hanyar da za ta tsabtace kuma ta sa-ido a harkar zirga-zirgar fasinjoji musamman na kasa da kasa. Lallai ne a sanya tsaro sosai a filayen jiragen saman kasar nan domin a tabbatar wani mai dauke da cutar nan bai shigo cikin kasar nan ba tare da sani ba. Sannan Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Lafiya ta Kasa su tabbatar sun tanadi wurare na musamman domin shirin gaggawa ba wai sai cutar ta bulla ba. Sannan ma’aikatan lafiya dukkan filayen jiragen saman kasar nan domin taya ma’aikatan filayen aikin sa-ido da kuma tantance mutane a kan wannan cuta.
Lokaci ya yi da jama’a za su dauki mataki wajen kula da lafiyar jikinsu musamman ta hanyar tsabtace hannaye da kaurace wa cin naman daji (Bush meat) sannan a rika tantance mutane a wuraren taruwar jama’a. Sannan duk ’yan Najeriyar da suka ji wasu alamu na cutar, kamar yawan zazzabi mai naci, su hanzarta zuwa cibiyar lafiya domin taimakawa wajen dakile yaduwar wannan cuta. Ya kamata a tanadi kudade na kada-ta-kwana. Dukkan wadanda suke aiki a kan iyakokin kasar nan su tabbatar sun dauki aikinsu da mahimmanci. A hada hannu waje guda domin kare Najeriya daga wannan cuta mai hadari.