✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ukraine ta nemi kasashen duniya su dauki mataki kan mamayar Rasha

Dmytro Kuleba ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matsaya ta bai-daya.

Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa da matsaya ta bai-daya, don kare kasarsu daga fadawa karkashin mamayar dakarun Rasha.

Yayin wani taron Majalisar Dinkin Duniya, Kuleba ya ce burin Rasha ba shi ne ta tsaya akan Ukraine ba, yana mai cewa tsunduma kasar ta Ukraine cikin yaki, zai janyo hatsaniya a duniya.

Ministan ya kuma yi gargadin cewa Rasha ta nuna alamun cewa a shirye take ta fadada wannan mamaya, lamarin da ya ce zai jefa rayukan dakarun Ukraine da na fararen hula da suka hada da yara da mata cikin mummunan hadari.

Tun a ranar Litinin Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ya tura dakaru dubu 150 kan iyakar Ukraine, ya rattaba hannun kan wata doka wacce ta ayyana yankunan Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu.

Ya kuma tura dakarunsa zuwa wadannan yankunan inda ya yi ikirarin cewa sun shiga ne don kare rayukan fararen hula.

Rasha ta kaddamar da hari kan Ukraine

Aminiya ta ruwaito cewa, tuni dai Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kaddamar da ayyukan soji a kan kasar Ukraine bayan share tsawon makonni ana zaman tankiya da kuma gazawar matakai na diflomasiyya tsakanin Rasha da kasashen Yammacin Duniya.

Shugaba Putin ya sanar da kaddamar da farmakin yayin wani jawabin ba zata da ya gabatar a gidan talibiji da misalin karfe 6 na safiyar ranar Alhamsi agogon Rasha, inda ya bukaci dakarun Ukraine su gaggauta ajiye makamansu musamman a yankunan da ke gabashin kasar ta Ukraine.

Putin, ya ce ya dauki wannan mataki ne domin kauce wa faruwar kisan kiyashin da mahukuntan birnin Kiev suka tsara aiwatarwa a yankin tare da kawo karshen take-take irin na tsokana da kasashe mambobi a kungiyar NATO ke yi wa Rasha.

Ministan tsaron kasar ta Ukraine Dmytro Kouleba ya ce Rasha ta tsara gagarumin shirin mamaye kasar, kuma tun a sanyin safiyar yau ta fara kai hare-hare da kuma jin karar fashewar abubuwa a wasu biranen kasar ciki har da birnin Kiev.

Tuni dai Ukraine ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga jiragen da ke jigilar fasinja.

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci tsagaita wuta a cikin gaggauwa, sai kuma shugaba Joe Biden na Amurka wanda ya yi tir da wannan farmaki na Rasha yayin da kungiyar tsaro ta NATO ke shirin gudanar da taron gaggawa kan lamarin a yau alhamis.

%d bloggers like this: