✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ubangiji ne madogarana (2)

“Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka…

“Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.” Karin Magana 3:5-6

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka. Barkanmu kuma da sake haduwa don ci gaba da nazari a kan Ubangiji ne madogaranmu. 

A kowace rana mukan yi shirye-shiryen harkokinmu na yau da kullum, wadansu ma ba sa iya yin barci sai sun ga cewa sun lissafa, sun kuma shirya harkokinsu na gobe. Yin shiri na da kyau kwarai da gaske amma idan mun sa komai cikin hannun Ubangiji Allah muka kuma dogara gare Shi cewa da ikonSa ne za mu ci nasara cikin shirye-shiryenmu. 

Karin Magana 16:1-3, Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce. Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji Yana auna manufarka. Ka roki Ubangiji, Ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.

Duk shirin da mutum ke yi ba tare da nufin Ubangiji ba, to, wannan a banza ne dalili kuwa shi ne ba mu san abin da zai faru a yanzu ko da jimawa ba, Ubangiji kadai ke da ikon sanin wannan. Shi ya sa yana da muhimmanci kwarai da gaske mu nemi nufinSa da jagorancin Ubangiji cikin rayuwarmu a koyaushe.

Bari mu ga misali da wani mai dukiya da Yesu Almasihu ya bayar cikin Littafin Luka 12:16-21. Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai dukiya ta yi albarka kwarai. Sai ya ce a ransa, ‘To, kaka zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina wadansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. Zan kuma ce wa raina, “Lallai ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagalina.”  Amma Allah Ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karbi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’ Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba ya kuma da wani tanadi a wurin Allah.” 

Haka rayuwar mutane da dama take a yau, mukan kwallafa ranmu ga tattalinmu ko mu ce arzikin da muke da shi, shin wa ke ba da arzikin? Wa kuma ke da ikon karba? Idan haka ne, me zai hana mu neman wanda ke da ikon tanadawa ya kuma karbe cikin kiftawar ido?

Kariya fa? Mun ga wadansu da sukan gina kariya kewaye da su, za ka gan su tafe da sojoji, ko ’yan-sanda da motoci masu (sulke da na) agaji, duk wadannan na nufin ba wanda zai iya taba rayuwarsu. Bari mu ga abin da Littafi Mai tsarki ke fadi game da irin wadannan mutane.

 Irmiya 17:5-8: Ubangiji Ya ce, “La’ananne ne mutumin da ke dogara ga mutum. Wanda jiki ne makaminsa. Wanda ya juya wa Ubangiji baya. Gama yana kama da sagagi a Hamada. Ba zai ga wani abu mai kyau yana zuwa ba. Zai zauna a busassun wuraren Hamada. A kasar gishiri, inda ba kowa. Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji. Wanda Ubangiji ne madogaransa. Shi kamar itace ne wanda aka dasa a bakin rafi. Wanda ke mika saiwoyinsa zuwa cikin rafin. Ba zai ji tsoron rani ba. Kullum ganyensa kore ne. Ba zai damu a lokacin fari ba. Ba zai ko fasa yin ’ya’ya ba.”

Zabura 20:7-8: “Wadansu ga karusan yakinsu suke dogara. Wadansu kuwa ga dawakansu. Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara! Za su yi tuntube su fādi. Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!” 

To ka ji, dogara ga karfi ko kariyar kanmu ba za su hana mutuwa ko asara ba, bari madogararmu ta zamana cikin Ubangiji da ke da iko bisa komai, gama zai aiko da mala’ikunSa su kare ka daga kowane irin bala’i. 

Za mu rufe da Zabura 62:5-12: Ga Allah kadai na dogara. A gare shi na sa zuciyata. Shi kadai ne Mai kiyaye ni, Mai Cetona, Shi ne kariyata. Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam. Cetona da darajata daga Allah ne, Shi ne kakkarfan makiyayina, Shi ne mafakata. Ya jama’ata, ku dogara ga Allah a kowane lokaci! Ku fada maSa dukan wahalarku. Gama Shi ne mafakanmu. Talakawa kamar shakar numfashi suke. Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma’auni, sam ba su da nauyin komai. Sun fi numfashi shakaf. Kada ku dogara da aikin kama-karya. Kada ku sa zuciya za ku ci ribar komai ta wurin fashi. In kuwa dukiyarku ta karu. Kada ku dogara gare ta. Sau daya Allah Ya fada, Sau biyu na ji, cewa Allah Yake da iko. Madauwamiyar kauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji, kake saka wa kowane mutum bisa ga ayyukansa.

Shalom!