Mahaifi wata daliba ya dauki hayar ’yan daba da makamai su kai wa malaminta farmaki a makarantar da take karatu.
Mahaifin dalibar ya kai ’yan dabar makarantar ne a cikin wata mota mara lamba da zimmar su lakada wa malamin duka domin su koya masa darasi saboda ya yi mata bulala.
- Daga Laraba: Tsakanin uwa da uba laifin waye lalacewar tarbiyyar ’ya’ya?
- Dalibai da ma’aikatan FGC Yauri sun kubuta
Zuwansu makarantar ke da wuya, sai mutanen suka fara zaro adduna suna barazanar za su aika malamain lahira a bainar jama’a.
Tuni dai ’yan sanda suka damke mahaifin, mai suna Abidemi Oluwaseun, tare da ’yan dabar da ya dauko, bayan shugaban makarantar ya kai musu kara.
Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce al’amarin ya faru ne ranar Talata a makarantar ’yan mata ta gwamnati ta Baptist Girls, da ke Idiaba Abeokuta a yankin Ota na jihar.
DSP Abimbola Oyeyemi ya ce mahaifin yarinyar ya amsa cewa shi ne ya dauko hayar mutum biyun su jibgi malamin, su koya masa darasi, saboda dukan ’yarsa da ya yi.
Ya kara da cewa an kwace motar da makaman da wadanda ake zargin suka kawo, su kuma ana bincikar su.
Ya ce ’yan dabar da mahaifin dalibar ya kai makarantar gwamantin sun hada da mai shekara 24 da wani mai shekara 25.
Jami’in dan sandan ya ce binciken da suka fara gudanarwa ya nuna yarinyar da wasu dalibai sun rika dauke hankalin sauran dalibai tare da aibata malamin a lokacin da yake koyarwa a cikin aji.
A sakamakon haka ne malamin ya sa aka fito da duk masu surutu a ajin, ya yi wa kowannensu bulala a matsayin ladabtarwa.
Ita kuma da ta je gida sai ta kai wa mahaifinta kara, shi ne ya kwaso ’yan daban da aka kama shi tare da su, bayan sun je sun tayar da hankula a makarantar.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya sa zurfafa bincike kan lamarin sannan a gurfanar da mutanen a gaban kotu.
A cewarsa, muddin aka bari mutane suka ci gaba da yin irin hakan, to za a samu tabarbarewar doka da oda.