Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama wani mutum da dansa bisa zarginsu da hada baki da kashe wani Bafullatani makiyayi a kauyen Gbagba Elewure da ke Karamar Hukumar Odede.
Wanda ake zargin mai shekara 45, mai suna Kolese Womiloji ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da al’amarin ya faru yana gida, yayin da dansa mai suna Taiwo Womiloji ke gonarsu.
“Na san Bafulatanin, a nan yake zaune a kauyenmu. Na sha yi masa gargadi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa ya daina kiwo a gefen gonata, to lokacin da abin ya faru shi dan nawa ya yi masa kashedi ya kauce daga gefen gonar, da ya ki sai ya hau shi da fada.
Dama akwai zoben tsafi a hannun dan nawa, koda ya rike shi gam sai ya mutu. Da na je gonar sai muka ciccibi gawar muka jefa ta a wata tsohuwar rijiya amma ba mu sare shi da addaba ba kamar yadda ’yan sanda suka fadi. Lokacin da na je wajen mutumin ya riga ya rasu, fatata hukuma ta yi mana sassauci,” inji shi.
Dansa Taiwo Womiloji mai shekara 25, ya bayyana wa Aminiya cewa tabbas ya doki Bafulatanin makiyayin da wani zoben tsafi da ke hannunsa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa. “Zoben yana hannuna fiye da shekara biyar kuma ban taba jarraba amfani da shi ba. Wani mutum ne ya ba ni shi, wanda ke taimaka min da maganin tsari. Daga baya na je wajensa in nemi taimako, aka ce mini ya rasu,” inji shi.
Ya ce a ranar da lamarin ya faru yana zaune a gonar mahaifinsa sai ya hangi Bafulatin yana kiwo a daura da gonarsa, ya yi masa magana ya ki bari sai ya riko shi da hannun da yake sanye da zoben, ya buge shi. Nan da nan ya fita hayyacinsa, inda nan take ya rasu.
“Ni kaina ban san haka zoben yake aiki ba, domin ban san zai iya kashe mutum ba,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa sun yi nasarar kama wadanda ake zargi da kashe Bafulatanin mai suna Abubakar Sidi Usman mai shekara 32, bayan da dan uwansa ya shigar da kara ga rundunar.
“Dan uwan mamacin mai suna Usman Bello ne ya shigar da kara a ofishinmu da ke Odede, inda ya ce kanensa ya fita kiwon shanu a yankin, bai dawo gida ba. Lamarin da ya sanya jami’in ’yan sandan yankin, CSP Ajayi Williams ya jagoranci ayarin jami’ansa suka shiga bincike, inda suka gano gawar mamacin an sassare ta da adda a cikin wata rijiya,” inji shi.
Ya ce bincikensu ya kai su ga kama mutum biyun, wadanda suka amsa laifinsu, suka kuma ce mamacin yana kiwo ne a daura da gonarsu, koda suka yi masa magana ya bar wajen ya ki kula su, sai suka dake shi da bulala ta tsafi; lamarin da ya sa ya fita hayyacinsa, kafin daga bisani su sassare shi da adda su kuma jefa gawar a rijiya.
Ya ce, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Mista Kenneth Ebrimson ya ba da umarnin a ci gaba da bincike. Ya yi gargadi ga masu daukar doka a hannunsu cewa rundunar ba za ta sarara musu ba.
Aminiya ta ji ta bakin Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyati Allah a Jihar Ogun, Alhaji Abdulmumini, wanda ya ce ba su ji dadin yadda lamarin ya kasance ba. Ya ce a koyaushe suna kokarin ganin an samu kyakkyawar fahimta a tsakanin makiyaya da manoma a jihar, inda ya yi fatar za a yi wa mutanen hukuncin da ya dace idan an same su da laifi, domin hakan ya zama izina ga na baya.