Daga karshe dai Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da dage haramcin shiga kasarta da ta kakaba wa ’yan Najeriya.
Hakan da zai share fagen dawo da sufurin jiragen sama tsakanin kasashen biyu wanda aka dakatar a watannin baya.
- Biyafara: Gwamnonin Kudu maso Gabas sun nesanta kansu da ’yan IPOB
- Masu kai wa ’yan bindigar Kaduna burodi sun shiga hannu
Tun a watan Maris din da ya gabata ne dai kasashen suka fuskanci tsamin dangantaka kan bukatar yin gwaje-gwaje a kai a kai wanda UAE ta bullo da shi, kari a kan gwajin cutar COVID-19 da Gwamnatin Najeriya ta tilasta yi ga matafiya.
Tuni dai kamfanin jiragen sama na kasar ta UAE wato Emirates wanda ya sanar da dakatar da zuwa Najeriya tun a watan na Maris ya sanar da dawowa tun a ranar 23 ga watan Yunin 2021.
Hakan dai ya biyo bayan yin gyaran fuska ga dokokin tafiye-tafiye da Kwamitin Kiyaye Annoba na Dubai ya yi, inda a yanzu za a bukaci ’yan Najeriya su gabatar da sakamakon gwajin cutar COVID-19 kawai.
Kamfanin Emirates a cikin wata sanarwa ya yi maraba da sabbin dokokin wadanda Kwamitin ya fito da su domin fasinjoji masu zuwa Dubai daga Najeriya, Afirka ta Kudu da kuma Indiya.