Jakadan Turkiyya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce nan ba da dadewa ba jiragen yaki marasa matuka da jirage masu saukar ungulu daga Turkiyya za su isa Najeriya.
Mista Bayraktar ya bayyana tallafin tsaro da Turkiyya ke bai wa Najeriya a matsayin wata nasara daga yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da kasashen biyu suka kulla a shekarar 2021.
- Luiz Lula ya sake zama Shugaban Brazil bayan fitowa daga gidan yari
- Ruftawar gada ta yi ajalin mutum 132 a Indiya
Ya kara da cewa, Turkiyya na shirin bai wa Najeriya duk wani nau’i na tallafi a kokarinta na dakile barazanar tsaro ta hanyar ba da horo a bangaren gogewarta da fasaharta.
A cewar Mista Bayraktar, yana mai alfaharin sanar da cewa, wasu dandali guda biyu na masana’antun tsaron Turkiyya, Bayraktar (TB-2) jirage marasa matuki da kuma (T-149) ATAK masu saukar ungulu za su isa Najeriya.
Mista Bayraktar ya ce sabbin kayayyakin kariyar na Turkiyya za su taimaka wa kokarin gwamnatin Najeriya tare da bayar da gudummawa sosai ga zaman lafiya, wadata da tsaron ’yan Najeriya.
Ya ce gwamnatin Turkiyya na kuma sa ran gwamnatin Najeriyar za ta mayar da martanin da suka dace kan harakokin tsaro ta hanyar daukar matakan da suka dace wajen yaki da yan ta’adda a Najeriya.
Dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Bayraktar ya ce yana matukar alfahari da cewa 2021 da 2022 sun kasance wani babban ci gaba a dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Najeriya.
Ya ce, a halin da ake ciki na karuwar huldar kasuwanci a yanzu, yana da yakinin cewa nan ba da jimawa ba Turkiyya za ta cimma burin da ta sa a gaba na dala biliyan 5 na hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Karamin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, ya ce Najeriya da Turkiyya sun samu ci gaba a fannin kasuwanci tun bayan ziyarar manyan jami’an kasashen biyu a shekarar 2021.