Hukumar Kula da Sadarwa ta kasar Turkiyya ta ci tarar shafin Twitter Fam dubu 33, (fiye da Naira miliyan tara) saboda zarginsa da kin cire wata farfaganda ta ’yan ta’adda.
Wannan ne karon farko da aka ci kamfanin Twitter tara, kamar yadda BBC ya bayyana.
Hukumomin Turkiyyar ba su bayar da cikakken bayani game da abin da farfagandar da ake magana a kanta ta kunsa ba, sai dai an fahimci cewa tana da alaka da wani shafi da masu boren siyasa ke sukar gwamnati.
Kawo yanzu kamfanin bai ce komai ba tukuna. Kuma wannan ba shi ne karon farko ba da shafin ke shiga matsaloli da hukumomin kasar.
A cikin watan Afrilun bana, an rufe shafukan Twitter da Facebook a kasar bayan wani umarnin kotu da ke hana mutane yada hoton wani mai shigar da kara da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Hakazalika, a watan Maris din bara, an bayar da rahoton rufe shafin na Twitter a kasar bayan Firayiministan kasar a wancan lokacin, Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin kawar da Twitter gaba daya.
Hakan kuwa, saboda wasu zarge-zarge ne game da jam’iyyarsa da aka rika yadawa ta shafin kafin zabubbuka.
Turkiyya ta ci tarar Tweeter kan yada farfaganda
Hukumar Kula da Sadarwa ta kasar Turkiyya ta ci tarar shafin Twitter Fam dubu 33, (fiye da Naira miliyan tara) saboda zarginsa da kin cire…