Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wata tunkiya mara jin magana. Labarin ya yi nuni ga yadda rashin jin magana ke zama hadari. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
A wani daji wanda akwai namun daji da dama, akwai wata tunkiya wacce ba ta cika jin magana ba.
A dajin akwai nau’o’in namun daji masu yawa, inda aka kayyade su. Namun dajin sun kunshi irin su karen daji da sauransu. A kan haka ne mahaifiyar tunkiyar nan ta gargade ta da kada ta kuskura ta rika tsallakewa zuwa wani bangare saboda hadarin yin haka.
Ran nan da wasa ya yi wasa, sai tunkiyar ta tsallaka zuwa daya gefen. Ba ta ankara ba sai suka yi ido biyu da karen daji, inda shi kuma ya rika murna ya samu abincin da zai karya. Ana cikin haka sai wani karen dajin ya sake fitowa suka yi wa tunkiyar zobe.
Ganin haka sai ta runtuma a guje, karnukan dajin biyu suna bin ta amma ba su kama ta ba har ta koma gida. Shi kuma daya daga cikin karnukan dajin bai bar bin ta ba.
Ganin haka sai mahaifiyar tunkiyar ta dauki sanda ta rafka wa karen dajin inda ya koma baya a guje, ita kuma tunkiyar ta shiga gida tana ta haki.
Daga nan ne mahaifiyarta ta nuna mata illar kin bin umarnin iyaye, a nan take tunkiyar ta gane kurenta da alkawarin ba za ta sake saba wa umarnin iyaye ba.