✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano

Aranar Talata mai zuwa 17 ga watan Afrilun 2018 ne 2018 za a yi bikin tunawa da marigayi Mallam Aminu Kano, wanda yake gogyaggen malamin…

Aranar Talata mai zuwa 17 ga watan Afrilun 2018 ne 2018 za a yi bikin tunawa da marigayi Mallam Aminu Kano, wanda yake gogyaggen malamin makaranta ne, kuma mashahurin dan siyasa, masanin al’amuran yau da kullum sannan  marubucin kagaggun labararruka na hikayoyi.   A yau Malam Aninu Kano ya cika shekara 35 da kwana 4 cifi-cif yana kwance a kabari.

 Kafin rasuwar Malam Aminu, a ranar Lahadi 17 ga watan Afrilu 1983, an dade ana cewa, Mallam Aminu ya rasu, ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, illah dai a ce mutuwa ba ta cimmasa ba har sai da Allah Ya kawo wa’adinsa, domin ko a 1982 lokacin da aka taya shi murnar cika shekaru 62 da haihuwa agidansa, sai da Malam ya yi tsokaci a kan masu yi masa kage da fatan mutuwa, har ya kira su da suna ’yan tsegumi, ya ce, “ana cew na mutu to ga shi na farfado, kuma zan yi magana.”

Allah Akbar! Hakika Najeriya ta yi rashin dan kishin kasa, wanda cike gurbin irinsa yana da matukar wahala, domin Mallam Aminu, Uba ne kuma mai matukar kula da al’umarsa da kuma ’yan siyasa, wanda a zahiri ya yi imani da tsari irin na adawa, wanda a cikin tsarin ya rayu har kuma ya koma ga Allah.

Tun lokacin da Malam Aminu ya kammala karatunsa, abubuwa hudu Malam ya so ya yi a rayuwarsa ta fuskar sana’ar zaman duniya, amma daga karshe babu wanda ya samu, amma sai dai aka ce masa, sai dai ya yi aikin koyarwa, shi kuma sam ba ya san sana’ar koyarwa, amma idan an duba za a ga cewa a aikin koyarwar ne Malam ya samu damar zama dan siyasa, ya kuma cimma duk wani burinsa da zai sharewa talakan kasar nan hawaye a kan ya ga lallai ya samu ’yanci, a haka ya rika ganawa da talakwa yana fada musu yadda za su san ’yancin su, cikin hikima su kuma yi karatu domin a rika damawa da su a sha’anin mulkin kasar nan, don haka a karshe dai Malam ya fada siyasa gadan gadan, kuma siyasar da bai taba tsammanin zai shige ta ba. amma sai ga shi ya shige ta har ya rayu a cikinta, ya kuma koma ga Allah, a cikinta. Malam Aminu ya shiga harkokin siyasa, ba domin ya samu mulki ko a mutu ko a yi rai ba, amma ya shiga domin ya cimma wasu buruka guda shida kamar haka:

(1) Ya shiga siyasa domin bin sahun ’yan kishin kasa masu gwagwarmaya da Turawa ’yan mulkin mallaka, domin samawa Najeriya ’yancin kai,

(2) Domin ganin talaka ya samu ’yanci da sassauci game da biyan haraji da jangali, domin ana musu kudin goro wajen biyan haraji tsakanunsu da masu arziki,

(3) Ya kuma koyawa talaka cewa a’a ko na ki, a lokacin da aka umarce shi ya yi noma a gandun Sarki, ba tare da an ba shi ko kwabo ba,

(4) Ya yi ko karin a tsame hanun sarakunan gargajya game da sha’anin kula da iko a kan ’yan Doka da kuma gidajen yari,

(5) Mallam Aminu shi ne mutun na farko a Arewa da ya matsa lallai sai an bai wa mata ’yanci a Arewa, kuma sai sun samu ’yancin jefa kuri’a a lokacin zabe, da kuma ba su dama su shiga harkokin siyasa da sha’anin mulki, a dama da su.

(6) Abai wa ’ya’yan talakawa dama su yi karatu kuma a bar su su rike mukamai na siyasa da na bangaren gwamnati.

Idan an duba za a ga cewa, duk wadannan manufofi na Mallam da ya yi ta kokarin sun tabbata to Allah Ya cika masa burinsa, domin tun kafin Allah Ya dauki rayuwarsa sai da ya ga cikar burin nasa. Duk wanda ya san Mallam Aminu Kano, musammanma wadanda suka yi tarayya da shi, a cikin shekaru fiye da 30 da ya yi yana hidimar siyasa, a kasar nan to sun san tunaninsa in garin Allah ya waye bai wuce abu daya ba , wato yadda za a kyautatawa zaman jama’a, talakan kasa ya san masu shugabancinsa kuma su ma su san da zamansa da kuma sanin abin da ke damunsa.

Ko 1979 abin da ya hanga ke nan lokacin da ya ji ‘yan Jam’iyar P.R.P suna ta korafi da jin zafin cewa, Jihohi guda biyu kacal suka samu wato Kano da Kaduna, a zaben da aka yi, amma Malam ya ce musu su yi hakuri Allah ba Ya ya yin wani abu  sai da dalili domin watakila Allah jarraba mu ya yi, wajen ba su jihohi biyu a cikin sha tara ko za su iya kwatanta gaskiya da adalci, domin kada ya ba su jihohin duka su handame dukiyar al’umma,

Wanan ke nan, watakila babu abin da ya fi tayarwa Malam hankali a rayuwarsa ta duniya, irin yadda yake ganin sauran jama’ar kasar nan suke daukarmu a matsayin wadanda ba mu san ciwan kanmu ba, ba mu da ilimin zamani, iyayanmu al’majirai ne ko kuma makiyaya koma-bayan sauran jama’ar kasar nan, musamman idan aka kwatanta mu da mutanen Kudu wadanda suka yi mana fintinkau wajen ilimin boko.

Hakika wanan shi ne dalilin da ya sa Malam ba ya saurarawa ko rangwanta wa duk wanda ya raina mu, musamman a lokacin da Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya yi yunkurin dawo da Hedikwatar kasar nan daga Legas zuwa Abuja a 1982, a lokacin da ya ji irin muggan kalamai da suka rika futowa daga bakunan wadanda ba sa so a taso, to da aka zo wannan fagen na kiyayya da cigaban arewa, duk da Malam yana Jam’iyar adawa to Malam ba ya shakka a yi ta ta kare domin kare martabar arewa.  

Sau tari in anzo irin wannan matsalar to zakaji yana cewa ba za’a hada kai damu ta kowacce hanya acuci wannan bangare na arewa mundun muna nunfashi. Wato a kullum irin tunanin Mallam kenan, Shin Yaya za’ayi mu iya zama da junanmu, mugane mai sanmu da dalilin da yake sanmu ko kuma kinmu da kuma ta yadda zamu zauna domin muci amfanin zaman tare.

An haifi Malam Aminu ne a Unguwar (Sudawa) cikin birnin Kano.   Mahaifinshi shi ne Alkali Yusuf, wani mashahurin Malamin addini, kuma Alkali a kotunan shari’ar musulunci a Kano. Marigayi malam Aminu Kano ya yi karatun Alkur’ani mai girma a wajen shehun malami, Malam Halilu, Malam Halilu shi ne Limamin Sarkin Kano Abdullahi Bayero a shekarar 1929 zuwa 1953. Ya halarci makarantar Ilimantari ta Shahuci da Middle School ta Kano tsakanin 1930 izuwa 1937, daga nan ya wuce Kwalejin Horar da Malamai ta Katsina inda ya kammala a 1942 sai aka tu rashi aikin koyarwa a makarantar horon malamai ta Bauci, a shekarar 1946 sai aka turashi kasar Ingila domin yin Kwas a (London Institute of  Education) tare da Alhaji Sa Abubakar Tafawa balewa, a can Baucin ne k ya hadu da mutane irins u Sa’ad Zungur da  Abubakar Tafawa balewa inda suka kafa kungiyar Bauchi General Improbement Union, kungiyar da suka rika amfani da ita wajen wayar da kan al’umma domin su san ’yancinsu. Yana Bauci har zuwa 1948 lokacin da aka mayar da shi Makarantar horas da malamai ta Maru a Lardin Usman M. Sakkwato. Mallam Aminu yaci gaba  da adawa da munanan manufofin Turawan Ingila, sakamakon haka sai aka kara tura shi Ingila domin sake yin wani kwas, amma jim kadan da dawowarsa, sai ya kafa kungiyar kare muradun malaman makaranta Northern Teachers Association (N.T.A), domin alokacin babu irin kungiyar a arewa, sai dai a Kudancin kasar kuma ya zama Sakataren Kungiyar.

Mallam Aminu ya ci gaba da tsaya kyam domin ganin talaka ya samu ’yanci, daga nan sai aka yi masa tayin aiki mai tsoka domin a rufe bakinsa aka ce zai zama Babban Edita a wata mujjalla ko kuma ya zama Akanta a ofishin sha’anin kudi, Mallam Aminu ya ki, sai aka kara yi masa tayin zama malamin koyar da harshen Hausa a Jami’ar Osfod dake Ingila nan ma ya ki.

A karshe Mallam Aminu ya rubuta Littafi mai suna (Kano Under Hammer) domin yin raddi ga turawa saboda sun hana mahaifinsa Alkali Yusufa zama Alkalin-Alkalai na Jihar Kano, duk da ya cancanta a ba shi, amma saboda Mallam yana adawa da irin tsarin su na mulkin mallaka sai aka hana shi, daga nan sai Mallam ya shiga wata kungiya mai suna (Jam’iyar Mutanan Arewa) wacce daga bisani ta rikide ta koma babbar Jam’iyar Siyasa a Arewa (NPC) amma kuma daga karshe sai wasu masu ra’ayi irin na Mallam a 1950 kuma ‘yan ta- kife ’yan gwagwarmaya, suka balle daga Jam’iyar wacce a wancan lokaci ta dauki hanyar zama babbar Jam’iya mafi shahara da girma a Arewa, sai suka kafa jam’iyyar NEPU. 

A ranar 8 ga watan 8, mutane 8  irin su Magaji dambatta OFR da Bello Ijumu da Abba Maikwaru Baballiya Manaja da sauransu.Daga nan sai Mallam Aminu ya ajjiye akin koyarwa kacokan, sannan ya fada siyasa ya kuma hade da ’yan gwagwarmaya irin sa a Jam’iyar (NEPU) duk da cewa Mallam Aminu ba da shi aka kafa Jam’iyar (NEPU) ba amma shigarsa da shugabantar jam’iyar da ya yi, ya sa ta yi farin jini da daukaka a zukatan talakawan Arewa.

Mallam Aminu sau uku yana tsayawa takara a Jam’iyar NEPU amma sai sau daya ya ci zabe, da farko a 1954 ya tsaya takara dan majalisar Tarayya amma ya sha kaye a hanun dan Masanin Kano Marigayi Alhaji Sule Maitama. A 1956 a nan ma ya kara shan kaye a lokacin da ya shiga zaben majalisar Dokokin Jihar Arewa.  A 1959 ne ya ci zabe, a zaben da ya kara shiga na majalisar Tarayya.   Bayan an rantsar da shi a majalisa sai aka ba shi mukamin mataimakin mai tsawatarwa na majalisa (Deputy Chief Whip).

Bayan sojoji sunyi juyin mulki na farko, Gwamnatin mulkin soja ta Yakubu Gowon ta ba shi mukamin Kwamishinan Lafiya wato Minista daga 1967 zuwa 1974.  Shekarau 12 bayan da Gwamnati Obasanjo, ta dage takunkumin siyasa, sai Mallam da wasu ’yan kishin kasa suka kafa kungiyar siyasa ta (National Mobement) suka karade kasar nan lungu da sako domin ganin al’umma sun dage sai an dawo da mulkin dimokuradiyya, a karshe kungiya ta rikide ta zama Jam’iyar Siyasa (NPN) aka nada Cif Akinloye ya zama shugaba na kasa da Mallam Aliyu Makaman Bida a matsayin sakatare na kasa. Wannan lamari bai yi wa Mallam dadi ba, da masu ra’ayi irin nasa.

An yi wa Mallam haka ne domin a hana sa yin takarar shugaban kasa, domin kowa ya yi imani da cewa Mallam Aminu dan ra’ayin rikau da kishin al’umma ne, domin in har ya zama shugaban kasa to wata ran za a iya ganinsa a titi rike da kwali ya daga sama tare da talakawa suna zanga-zanga kin amincewa da duk wani kuduri in majalisa ta zartar wanda ba alheri ba ne ga talaka, don haka sai ya balle ya kafa Jam’iyyar PRP tare da wasu ‘yan takifen siyasa (radicals), irin su Edward Ikem Okeke da Sam Ikoku da Micheal Imodu da sauransu.

Mallam ya zama dan takarar shugaban kasa na PRP a 1979 amma bai samu nasara ba. Jam’iyyar PRP ta samu gwamnoni buyu ne wato (Kano da Kaduna).

Hakika ’yan Najeriya ba za su taba mantawa da irin gudunmawar da Mallam ya bayar ba, domin ganin Najeriya ta ci gaba, kuma talaka ya san ’yancinsa.

Mallam shi ne dan takara na faro a siyasa da ya zabi mace a matsayin mataimakiyarsa a zaben shugaban kasa a 1983, Misis Bola Ogunbola, amma Allah Bai sa zai ga zaben ba, sai Allah Ya karbi rayuwarsa.

Idan kuma aka zo batun ilimin addini da na boko, Mallam shi ne ya fara assasa makarantar Islamiyya wacce take kunshe da koyarwar addini da na boko, bayan da ya kai wata ziyara kasar Sudan ya ga yadda aka tsara koyarwar boko da addini a waje daya.  

Ta fuskar karatun boko kuwa, Malam ya yi kokari wajen ganin duk wadanda suke tare da shi da ba su yi karatun zamani ba, sai da ya koya masu karatu da rubutu.  Bayan da Malam ya rasu, an yi wadansu abubuwa don tunawa da shi kamar haka: Malam Anminu Teaching Hospital da Malam Aminu Int Airport da Aminu Kano Way da Cibiyar nazari da binciki a kan harkokin Siyasa (Mubayya House) da ke gidan Malam Aminu da dandalin Malam Aminu a Jigawa, sai kuma Aminu Kano Crescent Wuse 2 Abuja.

A kodayaushe Malam ya kan amabaci wasu mashahuran mutane kamar Usman danfodiyo da Mahatma Gandi, da cewa irin yadda suka yi gwagwarmaya ita yake kwaikwayo.

Malam Aminu ya rasu a ranar Lahadi 17 Afrilu 1983 a gidansa da ke Unguwar Gwammaja cikin Birnin Kano.

Ya rasu ya bar gida daya da gona daya da mota daya da  mata daya Hajiya A’isha da ‘yarsa daya Hajiya Maryam.

Malam Aminu ya sha fadin cewa ko ya mutu to bai bar komai a duniya ba, sai abin da zai tabbatar da mutuncin Talakan kasar nan.

Ado Musa Unguwar Goje Unguwar kaura Goje Kano 08069186916