Janar Yakubu Gowon shi ne shugaban ƙasar Najeriya na uku.
Shi ne mutum mafi ƙarancin shekaru da ya mulki Najeriya, inda ya zama shugaban ƙasa ya na da shekaru 31 da watanni tara a duniya.
Kuma shi yafi kowa daɗewa kan karaga cikin waɗanda suka mulki Najeriya sau ɗaya, domin kuwa ya shekara tara a kan gadon mulki daga 1966 zuwa 1975.
Tuna Baya: Tarihin shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Aguiyi Ironsi
Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa
A zamaninsa ne jihar Gabas ta ɓalle inda ta zama ƙasar Biafra.
Shi ya jagoranci yaƙin shekaru uku na dawo da Najeriya ƙasa ɗaya. Kuma bayan da aka samu nasara ya shelanta cewa babu wanda ya sha kayi kuma babu wanda ya yi nasara a tsakanin ɓangarorin biyu.
A zamaninsa tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa kuma ya yalwatawa al’umma da ayyukan cigaba da kuma jiƙa maƙoshin ƴan ƙasa ta hanyar ƙarin albashi da alawus-alawus.
Sai dai kuma ƙusoshin gwamnati sun yi sama-da-faɗi da dukiyar al’umma a zamanin mulkinsa.
Bayan da kuma ya karya alƙawarin da ya ɗauka na miƙa mulki ga farar hula, sojoji ƴan uwansa sun yi masa juyin mulki cikin ruwan sanyi a shekarar 1975.