Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya na farko.
A kan sa aka fara shugaba mai cikakken iko na farar hula sai dai ya na fara wa’adin mulkinsa na biyu sojoji suka yi masa juyin mulki.
A tsawon shekaru huɗu da wata ukun da ya yi ya na shugabancin Najeriya ya sha fama da adawar siyasa daga sauran jam’iyyu.
Tuna Baya: Tarihin shugaban ƙasar Najeriya: Janar Olusegun Obasanjo
Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Murtala Muhammad
Kuma Najeriya na cikin matsin tattalin arziki sakamakon karyewar farashin man fetur a kasuwar duniya.
Duk da haka jami’in gwamnatinsa sun yi facaka da almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Sai dai shi ana yi masa kallon mutumin kirki amma wanda ya kasa hukunta waɗanda yake tare da su.