✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tun daga makaranta na fara siyasa – Abubakar ’Yantumaki

An samu matasa da dama sun fantsama cikin harkokin siyasa a wannan kakar siyasa ta bana. Aminiya ta tattauna da matashin dan siyasa a Jihar…

An samu matasa da dama sun fantsama cikin harkokin siyasa a wannan kakar siyasa ta bana. Aminiya ta tattauna da matashin dan siyasa a Jihar Katsina, Abubakar Usman, wanda yake takarar Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar PRP. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Kwamared Abubakar Usman ’Yantumaki, An haife ni a garin ’Yantumaki a Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina, ranar  9 ga Yuli,n 1989. Na shiga makarantar firamare ta Model da ke garin ’Yantumaki a 1995, na kammala a 2001. Sannan na wuce makarantar sakandare ta jeka ka dawo ta garin ’Yantumaki a 2001, inda na kammala 2004, inda na wuce zuwa makarantar kwana ta Katsina College Katsina, a shekarar 2004; na kammala a 2007. Na samu nasarar wucewa Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsin-ma a shekarar 2007, na kammala a shekara ta 2010.

Yaushe ka shiga siyasa?

Na fara siyasa tun daga makaranta, inda na zama Sakataren Kudi na kungiyar Dalibai ta BIOSA. Bayan haka kuma na taba zama Babban Sakatare na Kungiyar Daliban Jihar Katsina (NAKATSS). Bayan na kammala karatu, na yi alaka da kungiyoyi masu yawa, inda wasu daga ciki na rike makamai, kamar:

A kungiyar Youth Enlightenment and Social Justice Foundation, na samu nasarar zama shugaba na shiyyar Katsina. A kungiyar Intellectual Young Leaders Network, na zama shugaba na Jihar Katsina. A kungiyar National Youth Council of Nigeria, na zama Jami’in Hulda da Jama’a na Karamar Hukumar Danmusa. A kungiyar Bunkasa Garin ’Yantumaki, na zama Sakatare. Na zama Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kungiyar Not Too Young to Run ta Jihar Katsina.

Yanzu wace kujera kake takara kuma me ya sa ka shiga takarar?

Ina takarar dan Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina daga mazabar Karamar Hukumar Danmusa. Dalilin da ya sa na fito takara shi ne, domin ci gaban al’ummar karamar hukumata da jihata baki daya.

Idan Allah Ya sa ka yi nasara, mene ne kudirorinka ga al’umma?

Insha Allahu zan yi kokarin samun hadin kan al’ummata don jin bukatunsu, wadanda zan kai a majalisa, wadanda suka shafi korafi, bincike, kasafin kudi da doka. Wadanda za su taimaka wajen inganta ilimi na addini da na boko da kiwon lafiya da noman rani da na damina da kuma bangaren tsaro.

Ta yaya za ka samu nasarar cika alkawurran?

Ta hanyar samun hadin kan al’ummata, domin sau da yawa wadansu al”ummar su suke kawo matsaloli. Ta hanyar taya ni da addu’a da kuma ba ni hadin kai wajen tafiyar da harkokin mulki za a samun nasara.