Hukumomin tsaro a jihar Kano sun tabbatar da rasuwar mutum hudu bayan fashewar wani abu da ake zargin tukunyar gas ce a unguwar Sabon Gari da ke Kano a safiyar Talata.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce an gano gawarwakin mutum hudu kuma jami’an tsaro na kokarin gano ko akwai ragowar mutane a cikin baraguzan ginin da iftila’in na safiyar Talata ya shafa.
- FCC ta kama Akanta-Janar, Ahmed Idris kan zargin almundahanar N80bn
- Hukumar ’Yan sandan Najeriya ta yi wa Magu karin girma
“Ba bom ba ne, tukunyar gas ce ta fashe; akwai wani mai sana’ar walda da gas a nan, shi ne wanda abin ya fara kashewa.
“Zuwa yanzu an gano gawar mace daya da maza uku kuma duk hukumomin tsaron da ke Jihar Kano sun zo nan,” kama daga sojojin kasa, sojojin sama, DSS, da sauransau.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya ce “za mu fadada bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.”
Lamarin ya faru ne a Titin Aba daura da Titin Kotu da ke Sabon Gari, wanda kawo yanzu ake ci gaba da gudanar aikin ceto.
An fitar da gawarwaki
Tun da farko, ganau sun shaida wa Aminiya cewa an fitar da gawara akalla mutum uku, ciki har da wani mai sana’ar walda a gaban makarantar firamare ta Winners daga cikin wadanda abin ya ritsa da su.
Wanin mazaunin unguwar ya yi ikirarin cewa ya ga lokacin da abin yi tashi da wani mutum da ke tafiy a akan layin — abin da wasu ke zargin dan kanar bakin wake ne — zargin da babu tabbaci a kai
Shaidu sun tabbatar wa Aminiya cewa ginin da ke wurin da abin ya yi bindiga ya ruguje gaba daya.
Tuni jami’an tsaro da Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da takwarorinsu na Jihar Kano suka isa wurin suna gudanar da aikin ceto.
Bidiyon wurin da abin ya faru ya nuna dandazon mutane na taimakawa wajen aikin ceto daga baraguzan wani gini da abin ya shafa.
Ko a bara an samu makamanciyar wannan musiba inda wata tukunyar gas ta fashe a Unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon, wadda ta yi sanadiyar jikkatar mutane uku.