Alkaluma na nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Gari da ke Kano a yanzu sun kai mutum tara.
Da safiyar Talata ce dai wani abu da ’yan sanda suka ce tukunyar gas ce ta fashe a kusa da wata makaranta inda ya jikkata mutane da dama, wani kuma ya mutu nan take.
- Hajjin Bana: NAHCON ta soma tantance kamfanonin da za su yi jigilar maniyyata
- An gano gawar mai kiwon macizai 124 a gidansa
Ma’aikatar Jin-kai ta Tarayya ce ta tabbatar da alkaluman, lokacin da take ayyana zuwan Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed a wajen fashewar.
Tun da farko dai ’yan sanda a Jihar sun tabbatar da mutuwar mutum hudu a wajen.
Ma’aikatar ta ce, “Ya zuwa yanzu, an gano gawar mutum tara daga cikin baraguzan ginin da suka danne mutane a kusa da wata makaranta firamare da ke titin Aba Road a Sabon Gari, sakamakon fashewar tukunyar gas.
“Shugaban NEMA, Mustapha Habib Ahmed ya je wajen kuma ya jagoranci aikin ceto mutane.
“Yanzu haka NEMA na jagorantar aikin ceto a wajen da hadin gwiwar sauran hukumomi masu aiki irin nata,” kamar yadda Ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter.