✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tukin Keke-Napep ya yi mini komai’

Shamsu Sunusi wani matashi ne da ya kwashe shekara uku yana yin aikin haya da babur mai taya uku wanda aka fi sani da suna…

Shamsu Sunusi wani matashi ne da ya kwashe shekara uku yana yin aikin haya da babur mai taya uku wanda aka fi sani da suna Keke-Napep a Abuja.
Ya ce duk da sana’ar akwai rufin asiri musamman ga matashi mai tuka irin wannan abin hawan. Hakazalika, su ma masu shi wadanda suke bayar wa a yi musu haya suna cewa suna samun abin sawa a bakin salati.
Wannan matashi ya ce duk da yawancin masu irin wannan sana’a na tuka wannan keke mai taya uku, sun taba yin haya da babur wato aikin acaba, sai dais hi ya ce shi bai yi acaba ba, amma ya dage ya rike aikin na sa bil hakki da gaskiya domin yana son ya samu ci gaba har ya iya kuma ya fara jan motar tasi a birnin Abuja da zuwa wasu birane.
Kodayake, ya ce shi yana tuka Keke-Napep ne wacce take zuwa da injin dizel, amma idan injin din ya yi sanyi ya fara gajiya, suna sayen injin Mota Nissan Micra su yi dabara su sanya wa keken kuma yana zama daram don su yi aiki da shi.
Har ila yau, ya kara da cewa wani makanike  ne a garin Funtuwa ya fara wannan aikin, inda ya samu daukaka ya musanya sana’arsa ta gyaran mota ya koma sana’ar cire tsohon inji don musanya shi da na mota sannan a sa kundun giya da kuma tankin man fetur mai cin lita 50 da batirin mota.
Ya kara da cewa wannan ya sa harkar ta su ta ci gaba, sai dai bambancin su da mai tuka mota shi ne su suna sanya giya ne ta hannun hagu, mai mota na sanya giya da hannun dama, sannan kuma kanbun tukin su shine kan babur irin na mashin ne ba sitiyari irin na mota ba.
A karshe Shamsu ya ce suna ba masu wannan Keke-Napep tsakanin naira 1,500 zuwa naira  2,000 a kullum.